Ta yaya za mu fahimci sanarwar da aka bayar da rahotanninta sosai da ta fito daga Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen China da ke cewa “Idan yaki abinda Amurka ke so, yakin haraji, ko na kasuwanci ko ma wani nau’i na yaki, a shirye muke ko a mutu ko a yi rai.”
Da yawa sun fassara wannan a matsayin ta’azzarar yakin cacar baki, daga bangaren China. Sakon da ba a saba gani ko jin irin sa ba da ya fito daga Ma’aikatar Harkokin Wajen China kai tsaye, an yi ta maimaita shi a kafafan yada labarai da ma shafukan sadarwa na yanar gizo a fadin duniya.
A takaice, wannan ba shi ne hargowar da muke yawan ji ko gani daga Ma’aikatar Tsaro, Global Times, ko daya daga cikin manyan jami’an diflomasiyya da ba ma sa magana ko suke yi bisa umarnin wasu kusosi da ke nesa.
Kazalika, sakon na da karfi sosai duba a yadda a lokacin zaben Amurka ‘yan watannin da suka gabata, sako a hukumance da aka fitar daga China da ma rahotannin da aka bayar a kafafan yada labarai na gwamnati sun dan sararawa Washington, suna jira su ga irin takun sakar Trump.
A yanzu a bayyana yake karara sabuwar gwamnatin Amurka na matsa lamba ga China, wannan sanarwa ta kai tsayi na nuni ga cewa an cire wannan sassauci, a kalla dai a an magantu.
Za mu iya kuma yin mamakin ko wannan na wani muhimmanci ga Beijing, wanda zai iya saka ta fara shirin shiga matakin yin fito na fito da Amurka.
Idan ficewar Amurkawa daga Ukraine zai bawa Amurka damar mayar da hankali kacokan kan China, kamar yadda wasu ke hasashe, to wannan lokaci ne na Beijing da ta bude kwanji ta nuna tsayin daka da nuna ta shirya tsaf don yin yaki da Amurka.
A daya bangaren kuma, wannan mataki ya dace da ra’ayin Beijing a wannan zamani, China ta dawo tsakiyar duniya a matsayin babbar kasa, wadda ke shaida yadda duniya mai manyan kasashe da dama ke tasowa.
A gefe guda, Trump a lokuta da dama ya bayyana amfanin aiki da lra idan aka zo batun Rasha, yana yawan ambatar yiwuwar fara yakin duniya na uku idan har aka lalata dangantaka.
Wannan na samar da yanayi mai muhimmanci a yayin da Trump ke kokarin warware shirin yakin da Biden ya yi da Rasha: shugabannin Amurka sun yi alkawarin kassara Rasha da lalata tattalin arzikinta.
Amma har yanzu, shugaban kasar Amurka na tattaunawa don yin sulhun da zai tabbatar da nasarar Rasha, kuma yana yin hakan ba tare da kawayensu ko ma Ukraine din a kan teburin tattaunawar ba.
A yayin da Trump ke nufar China, 2025 na iya fada wa yakin Cacar Baki
A yayin da Amurka ke baya a yakin kasuwancin, Zababben Shugaban Kasa Trump ya tsokanin babbar kasar ta nahiyar Asiya. Amma shin wa zai yi nasarar wannan yaki?
Darasin da China ta dauka a bayyane yake karara: ian Trump na tsoron yakin gama-gari da Rasha, Idan Rasha ta gagari NATO, ta gagari Ukraine, Turai da Amurka, kuma tattalin arzikinta ya jurewa duk wani irin hari, to ai China ma da ta fi Rasha karfin tattallin arziki da na soji za ta iya tsallake duk wani matakin kalubalantar ta da Trump ai yi.
A shekarar da ta gabata, akwai amincewa d ahadin kai a Beijing cewar wa’adin mulki na biyu na Trump zai fifita bukatun China.
Domin tabbatar da hakan, akwai wadanda suka damu cewa warware rikicin Ukraine zai ‘yantar da Washington ta mayar da hankali kan China.
Amma za a iya cewa Amurka na amfani da yakin don lalata lakar China da Turai.
Ana hakan kuma, gwamnatin Biden ba ta tsagaita ba wajen daukar matakan adawa da China inda har aka kai matakin da aka kusan gwabza yaki a 2023, wanda ya bukaci daidaitawa. Kuma a lokaci guda an fahimci cewar manufofin Amurka a Ukraine za su ruguje.
Mutum na iya muhawarar cewa 2023 ta zama shekarar rashin nasarar manufofi, ta fito da takaituwar karfin ikon Amurka a fili wajen kokarinta na zama kwaya tilo da ke fada a ana ji a duniya, shekarar da rikici ya biyo bayanta a tattalin arzikin China da karyewar wasu masana’antun fasahar kere-kere na Amurka.
Haka kuma, manufofin Biden sun rushe. A yayin da dawowar Trump na iya bawa Amurka damar sauya dabaru, amma su ‘yan China sun yi amanna da cewa ma shi Trump zai zama mafi rauni sama da wanda ya gada, a wajen samun goyon bayan kalubalantar China a duniya.
Sun yi tunanin zai janyo rarrabuwar kai da rikici a gwamnati a tskanin kawayen Amurka da ma a cikin Amurkan kanta kuma zai iya kulla alakar kasuwanci, kamar dai yadda aka gani a lokacin mulkin trump na farko.
Saboda shi yakin kasuwanci na azabtar da Amurkawa sosai, kuma ko ba jima ko ba dade, abokan Trump za su hadu da masu jefa kuri’a wadanda suke son zmaan lafiya da saukar farashin kayayyaki kamar yadda ya yi musu alkawari.
Trump ya toshe kasuwancin China a fannoni masu muhimmanci
Shugaban na Amurka a baya ya kara yawan haraji da kashi 10 kan dyukkan kayayakin da ake shiga da su kasar daga China.
Tabbas, idan ‘yan jam’iyyar Republican suka rasa rinjaye a Majalisar Dokoki, dawowar Trump a karo na biyu zai zama kamar rashin nasara ta biyu.
A yayin da Trump bai bayyana aniyarsa a fili gaba daya ba, Beijing na kallon Amurka na amfani da dabaru uku a lokaci guda. Ta farko ita ce zai iya ci gaba da kalubalantar China ta hanyar kasuwanci.
Amma wannan na iya kawo hatsarin janyo yakin tattalin arziki da zai kora China ta kalubalanci dalar Amurka.
Wannan na iya kuma kai wa ga yaki gaba da gaba, duba da yadda karfin soji da na tattalin arzikin Amurka na doron dala ne a matsayin ta na kudi mafi karfi a duniya.
Dabara ta biyu ita ce yadda Trump na iya amfani da ja da baya zuwa ga karfin iko karami, Sabon Salon Mamaya na Monroe, kamar yadda wasu matakansa suka nuna, inda zai dawo ga fagen Yammacin duniya da ake fifita Amurka.
Wannan na iya samun tallafi daga kalubalantar Greenland da Canada, duba ga darajar Arewacin Duniya idan aka kalli matsalar sauyin yanayi.
A yayin da hakan ke faruwa, dole China da Rasha su samar da matsaya musamman a Tsakiyar Asiya, wanda fadin sa da sauki amma aikata shi ke da wahala, duk da cigaban da bangarorin biyu suka samu ta hanyar aiki tare, a aikin ‘Belt Road’, BRICS, da Kungiyar Hadin Kan Kasashen Shanghai.
Dabara ta uku ita ce amfani da tattaunawa, inda yake sa ran zai samu irin wannan dama sosai daga China, ciki har da bayar da kariya ga dala, tattalin arzikin Amurka, da biyan bukatun Amurka a kasashen Latin, sannan kuma yana karfafa gwiwar zuba jarin China da samar da kayayyakinta a Amurka, tare da danne Turai kamar yadda yake yi.
Wannan mataki na ingiza Beijing tare da girgiza Turai, kuma shi ne mafi cim mawa a tsakanin dabarun uku kafin majalisar Dokoki ta koma hutu.
Bisa adalci ma za a iya cewa China ta fahimci wadannan dabaru da hanyar da za a bi don bullewa, kuma tana da shirin tunkarar kowanne.
A yanzu dai, nuna damuwa ko yin kururuwa ba su ne abinda ya kamata China ta yi ba, wanda da ma hakan trump ke son gani.
Abu na karshe da yake son ji shi ne kasar da ta fi Rasha karfi ta shirya gwabza yaki. Kuma ba kamar Canada, Mexico, Panama da Colombia ba, China ba za ta bari a zalunce ta ba.