9 awanni baya
Dan wasan gaba na Liverpool da Portugal, Diogo Jota, da ɗan uwansa sun rasu a hatsarin mota a arewa maso yammacin Spain, in ji 'yan sanda, makonni bayan da tauraron ɗan wasan ya yi aure.
Hukumar Civil Guard ta tabbatar da cewa wata mota ta kauce daga babbar hanya a ƙaramar hukumar Cernadilla, a lardin Zamora na arewa maso yammacin ƙasar, inda aka tabbatar da mutuwar Jota da ɗan’uwansa, Andre Felipe.
Firaministan Portugal, Montenegro ya ce, "Labarin mutuwar ɗan wasa Diogo Jota, wanda ya ɗaukaka sunan Portugal sosai, da kuma ɗan’uwansa, abin mamaki ne kuma abin takaici.
“Ina miƙa ta'aziyyata ga iyalansu. Wannan rana ce ta baƙin ciki ga wasan ƙwallon ƙafa da kuma wasanni na ƙasa da na duniya."