Alakar Turkiyya da Afirka ta habaka tsawon shekaru inda ta zama mai amfanar juna, mai tushen hadin kai, musayar albarkatu da girmama ‘yancin kasashe.
Dorewar samar da manufofin kasa da ci gaba da yin su na Shugaba Recep Tayyip Erdogan, sun zama masu mauhimmanci wajen habaka alaka a fannonin tattalin arziki, ayyukan soji da diflomasiyya.
Taron da aka kammala na Antalya Diflomasiyya da a birnin Turkiyya mai sunan Taron ya zama wata babbar cibiya ta yin murna da habaka wannan dangantaka, inda aka samu halartar shugabannin kasashen Afirka da yawa da ma sauran sassan duniya, kuma an samu damar gana wa da Shugaba Erdogan da gudana da kananan taruka a tsakanin kasashen da Turkiyya.
“Na yi gana wa mai matukar amfani da shugaba Recep Tayyip Erdogan, wadda a ciki muka karfafa aniyarmu ta inganta dangantakar da ke tsakaninmu, bunkasa kasuwanci, da lalubo hanyoyin hada gwiwa a bangarori daban-daban.
Ina mika godiyata ga Erdogan saboda karbar mu da girmama bakin.” Shugaba Julius Maada na Saliyo ya fada.
Ga Sudan, kasar da ke fama da mummunan yaki a tsawon shekaru biyu, Turkiyya da babbar rawar takawa wajen farfado da zaman lafiya da ake gina kasar.
Ministan Harkokin Wajen Sudan Ali Youssef ya jaddada cewa Shugaba Erdogan ya gana da Shugaban gwamnatin Rikon Kwarya ta Sudan Abdulfatah Al Burhan, inda tattaunawarsu ta mayar da hankali kan alakarsu da kokarin da suke yi na kawo karshen rikicin kasar ta arewacin Afirka.
Erdogan ya bayyana aniyar Turkiyya ta goyon bayan sake gina Sudan da dawo da al’amura kamar yadda suke a baya a kasar. Ya yabawa fadaddiyar alakarsu tare da sake jaddada kudirin Ankara na samar da lumana a Sudan tare da kare martabar iyakokinta.
“Mun yarda da hikimar shugaba Erdogan kuma muna jiran ya ci gaba da shiga tsakani. Da yardar Allah, za a samu sakamako mai kyau.
Turkiyya na yin dukkan kokarinta na taimaka wa Sudan ta samu zama lafiya ta hanyar diflomasiyya, kuma za ta kasance daya daga cikin kasashen da za su taka rawa wajen sake gina Sudan,” in ji Youssef.
Tabbacin bayar da taimako daga Turkiyya na zuwa a lokacin da a makonnin nan sojojin Sudan suka fatattaki mayakan RSF, inda sojoji suka kame wasu yankuna masu muhimmanci, ciki har da Khartoum da gari makocinsa na Omdurman.
Shugaba Hassan Sheikh Mohamud na Somalia, wani babban aboki na Turkiyya ya gana da shugaba Erdogan don habaka alakarsu.
A baya bayan nan Turkiyya ta shiga tsakani an samar da zaman lafiya tsakanin Somalia da Ethiopia, inda aka kawo karshen takaddamar da aka shiga bayan sanya hannu kan yarjejeniyar amfani da tashar jiragen ruwa da Addis Ababa ta yi da yankin Somaliland da ya balle.
“Ina tunanin tsarin hadin kan da Turkiyya ke bi ya fi karko da zama mai dorewa sama da tsarin da kasashen Yamma ke bi,” in ji karamin Ministan Harkokin Wajen Somalia, Ali Mohamed Omar, a tattaunawar sa da TRT Afrika.
Ya kara da cewa sabanin manyan kasashen Yamma da ba sa girmama kawayensu, tsarin Turkiyya ya zama mai mu’amala da jama’a maimakon shugabanci.
Fadada dangantaka
Alakar Turkiyya da Afirka a bangarorin ayyukan tallafi da cigaba na samun gudanarwa daga cibiyoyi irin su Hukumar Hadin Kai da Cigaba ta Turkiyya (TIKA), Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Crescent, da ma’aikatar lafiya, wadda ke yin ayyukan cigaba a nahiyar.
Asusun Maarif na Turkiyya ma na taka rawa ta musamman, na bayar da gurbin karatu ga dubunnan ‘yan Afirka.
TIKA kadai na gudanar da ayyuka a cibiyoyi 22 a nahiyar, suna ayyuka kan fadada kiwon lafiya, ilimi, da tattalin arzikin.
“Muna jin dadin alakarmu da Turkiyya, kuma mun amfana sosai daga goyon bayan da suke bayarwa ga horaswa da gina mutane.
Sun bai wa dalibanmu da dama damarmaki ta hanyar tallafin karatu,” Dr Phenyo Butale, ministan harkokin wajen Bostwana ya fada wa TRT Afrika.
“Mu gwamnati ce mai buri da ke son gina tattalin arziki da ke bukatar wasu dabaru, kuma Turkiyya ta taka babbar rawa a nan.
Mun kuma ci gaba da hada kai a fannin makamashi mai sabuntuwa. Suna da kwarewa da cigaba, kuma muna son kwaikwaiyon irin wannan kwarewa tasu,” Butale ya kara fada.
Turkiyya ta kuma kara karfafa diflomasiyyarta, inda ofisoshin jakadancinta a Afirka suka karu daga 12 a 2002 zuwa 44 a 2022.
Adadin ofisoshin jakadancin kasashen Afirka a Ankara ya karu zuwa 38 daga kwaya 10 a 2008.
“Dole na yabawa Shugaba Erdogan saboda jagorancinsa, manufa da amanna da Afirka. Ya yi nasarar hadin kan Kudu Maso-Kudu,” in ji Samuel Okudzeto Ablakwa, Ministan harkokin wajen Gana.
Ablakwa ya yi nuni da karfin gwiwar shugaban Turkiyya na zuwa wajen da wasu suka gaza zuwa.
Ablakwa ya fada wa TRT Afrika cewa “Yana da karfin gwiwa game da abubuwa da dama da shugabannin duniya suka yi biris da su.
Yana bugar kirji ya aikata su a lokacin da ake fadin za a yi yaki. Ya ja hankali ga gaskiyar cewa akwai rikici da yawa a duniya, akwai rikice-rikice da dama a Afirka, kuma dole sai mun hade waje guda don neman mafita.”
Ministan Somalia Ali Omar ya kushe tsohon tsarin Afirka na cewa ana da tsaffin kawaye wajen magnace matsalolin da ke damun nahiyar.
“Manufofinsu sun karkata ga kwashe kadarorin Afirka suna amfanar da ‘yan boko. Turkiyya kuma na da kaunar jama’ar Somalia, ana ganin sakamakon karara. Muna godiya ga hakan,” in ji shi.
Ministan harkokin wajen Gambia Mamadou Tangara na da ra’ayin cewa Turkiyya na mu’amalantar kasashen Afirka da manufar cude-ni-in-cude-ka, tana karfafa amana a tsakanin kawaye.
“Turkiyya ta kasance kwakkwarar abokiya da ke girmama kawayenta da take mu’amala da su,” in ji su.
Habakar alaka tsakanin Turkiyya da kasashen Afirka na zuwa ne a lokacin da manyan Ƙasashen Yamma, ciki har da Amurka, Faransa da Jamus, ke fuskantar durkushewar karfin fada a ji, musamman a Yammacin Afirka.
Da yawan wadannan kaksashen na Yammacin Afirka sun kori dakarun Faransa da na Amurka tare da dakatar da alakar tattalin arziki da Yammacin duniya.
Bunkasar kasuwanci
Turkiyya ta so bu kasa kasuwancinta da nahiyar Afirka zuwa dala biliyan 50, kusan ninki 10 sama da yadda yake 2003 na dala biliyan 5.4, in ji mataimakin shugaban kasar Cevdet Yilmaz a watan Disamban bara bayan gana wa da Firaminista Samuel Ntsokoane Matekane na Lesotho a Ankara.
Yilmaz ya ce yawan kasuwanci tsakanin Turkiyya da kasashen Afirka 54 ya karu ninki bakwai tsakanin 2003 da 2023, inda ya kai biliyan 37.
Baya ga yunkurin samar da zaman lafiya a Sudan da Kahon Afirka, Turkiyya ta habaka karfin soji a kasashen Afirka da dama don taimaka musu wajen magance kungiyoyin ta’addanci.
Ta bayar da horo da taimakon sojoji a kasashe irin su Mali, Nijar da Nijeriya, da sauran su, baya ga jiragen yaki marasa matuka da ta sayarwa kasashen.
Ministan Harkokin Waje da Hadin Kan Kasa da Kasa na Mali Abdoulaye Diop ya ce kawancen kasashen Sahel na AES, sabuwar kungiyar da aka kafa kwanan nana da ta hada Mali, Nijar da Burkina Faso, ya mayar da hankali ga yaki da ta’addani duk da kalubalen da suke fuskanta daga kasashen Yamma.
Diop ya soki takunkuman da wasu kasashen Yamma suka saka musu. “A ‘yan shekarun nan, mun gano cewa wasu Ƙasashen Yamma na kokarin saka takunkuman hana kasashenmu samun makamai ga sojoji,” in ji shi a wajen wata tattaunawa a wajen Taron Diflomasiyya na Antalya.
“Wannan ne ya sanya muka juya baya zuwa ga kasashe irin su Turkiyya, China da Rasha,” ya kara yin bayani.
Ministan Harkokin Wajen Gambia Tangara ya furta irin wannan tare da alakanta hakan ga halayyar Yamma ga Afirka, wadanda masu nazari da dama ke kallo na mu’amala da su.
“Idan wata kasa na son kakaba dabi’u da al’adunsu a kan mu, za mu yi watsi da su, abu na farko mafi muhimmanci. mu ‘uan Gambia ne kuma ‘yan Afirka. Turkiyya na girmama dukkan kawaye,” Tangara ya fada wa TRT Afrika.
Wadannan dabaru sun kai ga gacin hadin kan da ya haura Afirka ma.
“Turkiyya, Gambia da Azerbaijan kawaye ne uku a Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC) da ke goyon bayan mu wajen tsaya ga ‘yan uwa maza da mata a Falasdin,” in ji Tangara.
“A duk lokacin da muka ga rashin adalci, za mu ƙi amincewa da shi. Su ma suna goyon bayan manufofin adawa da abubuwan da ake yi a Myammar don tabbatar da cewa an kare hakkokin ‘yan Rohingya,” in ji shi.