TURKIYYA
2 minti karatu
Ministan Shari'a na Turkiyya Yilmaz Tunc ya kare ɓangaren shari'a yayin da ake bincike kan Istanbul
Yilmaz ya yi watsi da zargin cewa akwai maƙarƙashiyar siyasa a shari'ar da ake yi wa Magajin Garin Birnin Istanbul Imamoglu, yana mai ƙarfafa cewa fannin shari'ar Turkiyya na cin-gashin-kansa, tare da yin kira ga duniya ta mutunta tsarin shari'a.
Ministan Shari'a na Turkiyya Yilmaz Tunc ya kare ɓangaren shari'a yayin da ake bincike kan Istanbul
Ο Τούρκος υπουργός Δικαιοσύνης, Γιλμάζ Τουντς. / AA
27 Maris 2025

Ministan Shari'a na Turkiyya, Yilmaz Tunc, ya yi jawabi ga manema labarai na duniya a Ofishin Shugaban Kasa na Dolmabahce, inda ya musanta zargin cewa matakan shari'a da aka ɗauka na baya bayan nan kan Magajin Garin Istanbul, Ekrem Imamoglu da wasu, suna da alaƙa da siyasa.

Minista Tunc ya soki ƙoƙarin da ake yi na nuna cewa binciken shari'a da ake yi yana da alaƙa da siyasa, yana mai jaddada cewa shari'ar Turkiyya tana aiki ne cikin 'yanci.

"Tun farkon binciken, wasu kungiyoyi sun yi kokarin matsa lamba ga hukumomin shari'a ba tare da sanin cikakken bayanin shari'ar ba, suna kokarin nuna cewa lamarin maƙrƙashiyar siyasa ce. “Muna musanta irin wadannan maganganun marasa kan-gado," in ji shi.

“A cikin ƙasar da ke bin tsarin doka, dole ne a magance zarge-zargen laifi a kotu, ba a kan tituna ba."

Tunc ya bayar da sabbin bayanai kan bincike biyu da Ofishin Babban Lauyan Jama'a na Istanbul ya fara, wanda ya shafi mutum 106, ciki har da Imamoglu.

Wani binciken ya shafi mutum bakwai da ake zargi da taimaka wa wata kungiyar ta'addanci, inda uku ke tsare a hannun hukuma, daya kuma yana karkashin kulawar shari'a.

Binciken na biyu ya shafi zarge-zargen cin hanci da almundahana da zamba, da tattara bayanai ba bisa ƙa'ida ba a cikin wata kungiyar laifi.

Daga cikin wadanda ake zargi 106, an kama 51, an sanya 41 karkashin kulawar shari'a, yayin da 14 suka tsere.

Ministan ya jaddada cewa binciken yana dogaro ne da rahotannin laifukan kudi da kuma binciken masu sa ido, yana mai musanta zargin cewa akwai katsalandan na siyasa.

"Tsarin shari'a zai tantance zarge-zargen da kariya, da kuma hujjoji cikin gaskiya, domin tabbatar da cewa gaskiya ta bayyana," in ji shi.

Tunc ya kuma soki abin da ya kira son kai da rashin adalci daga wasu kasashen duniya.

"Abin takaici, wasu maganganun da suka fito kwanan nan daga al'ummar kasa da kasa sun yi watsi da muhimmin ƙa'idojin bin doka.

“Muna musanta irin wadannan ra'ayoyi masu son-kai kan Turkiyya," in ji shi, yana mai nuna cewa shuwagabannin siyasa a kasashe da dama suna fuskantar binciken shari'a.

Ya yi kira ga hakuri da girmama tsarin shari'ar Turkiyya, yana rokon kasashen Turai su dauki matsaya mai daidaito.

"Girmama tsarin shari'ar cikin gida na wata kasa abu ne mai muhimmanci. Muna sa ran halayen da suka dace wajen jiran sakamakon binciken," in ji shi.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us