NIJERIYA
2 minti karatu
Gwamnatin Nijeriya ta yi gargaɗi game da yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwa a jihohi 30 da Abuja
Ministan Albarkatun Ruwa na Nijeriya, Joseph Utsev ya yi wannan gargaɗi ne ranar Alhamis yayin da yake gabatar da rahoto na shekarar 2025 kan Yiwuwar Aukuwar Ambaliyar Ruwa
Gwamnatin Nijeriya ta yi gargaɗi game da yiwuwar fuskantar ambaliyar ruwa a jihohi 30 da Abuja
A shekarar da ta gabata ambaliyar ruwa ta yi mummunar ɓarna a wasi jihohin Nijeriya ciki har da haddasa asarar rayuka / Reuters
11 Afrilu 2025

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi hasashen cewa za a fuskanci mamakon ruwan sama wanda zai haddasa mummunar ambaliyar ruwa a jihohi 30 da kuma Abuja babban birnin ƙasar.

Ministan Albarkatun Ruwa na Nijeriya, Joseph Utsev ya yi wannan gargaɗi ne ranar Alhamis yayin da yake gabatar da rahoto na shekarar 2025 kan Yiwuwar Aukuwar Ambaliyar Ruwa.

Ministan ya ce jihohin da ke fuskantar ambaliyar ruwa su ne Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross-River, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Neja, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Rivers, Sokoto, Taraba, Yobe, Zamfara da Babban Birnin Tarayya.

“Ƙauyuka 1,249 da ke ƙarƙashin ƙananan hukumomi 176 na jihohi 30 da Abuja suna fuskantar gagarumin hatsarin ambaliyar ruwa, sannan akwai ƙarin ƙauyuka 2,187 a ƙananan hukumomi 293 da ke fuskantar ambaliyar ruwa tsaka-tsaki,” in ji Minista Utsev.

Ya ƙara da cewa jihohin da ke fuskantar gagarumar ambaliyar ruwa sun haɗa da Abia, Benue, Lagos, Bayelsa, Rivers, da Jigawa.

A cewarsa, jihohin da ke gaɓar teku za su fuskanci ambaliyar ruwa sakamakon ƙaruwar ruwan sama da tasirin sauyin yanayi.

Ministan ya ce an fitar da wannan gargaɗi cewa tare da yin bayani dalla-dalla game da wuraren da lamarin zai shafa domin kauce wa samun gagarumar asarar rayuka da ta kayayyaki.

Joseph Utsev ya ce gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwa da sauran ɓangarori suna ɗaukar matakan rigakafi tare da ƙoƙarin ganin an kauce wa mummunan tasiri na ambaliyar ruwan.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us