NIJERIYA
2 minti karatu
An gurfanar da Ba'indiye da 'yan Nijeriya 12 a kotu kan zargin satar dizel na Dangote na N4bn
An gurfanar da wadanda ake zargin a gaban Mai Shari’a Deinde Dipeolu inda ake tuhumarsu da laifuka 16 da ke da alaƙa da haɗa tuggu, da karkatar da dizel ba bisa ƙa’ida ba, da kuma karɓar kuɗaɗe ta hanyar karkatar da dangogin fetur.
An gurfanar da Ba'indiye da 'yan Nijeriya 12 a kotu kan zargin satar dizel na Dangote na N4bn
Dangote / Dangote
11 Yuni 2025

Sashe na musamman mai kula da laifukan damfara na rundunar ‘yan sandan Nijeriya, SFU ya gurfanar da wani Ba’indiye da wasu mutum 12 ‘yan Nijeriya a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Lagos, kan zarginsu da haɗa baki wajen karkatar da dizel ba bisa ƙa’ida ba da kuɗinsa ya kai naira biliyan huɗu.

Dizel ɗin mallakin kamfanin Dangote ne.

An gurfanar da wadanda ake zargin a gaban Mai Shari’a Deinde Dipeolu inda ake tuhumarsu da laifuka 16 da ke da alaƙa da haɗa tuggu, da karkatar da dizel ba bisa ƙa’ida ba, da kuma karɓar kuɗaɗe ta hanyar karkatar da dangogin fetur.

Lauyan masu ƙara MY Bello ya shaida wa kotun cewa waɗanda ake zargin ma’aikatan kamfanin Dangote ne da kuma wasu kamfanonin da ke sufurin fetur daga matatar Dangote zuwa defo-defo ɗin kamfanin na Ibese da Obajana.

Mutum biyu ne ma’aikatan kamfabin Dangote, yayin da sauran suke aiki da kamfanonin irin su Arigen Integrated Limited, Obat Limited, Amaiden Energy Limited, Regal Gate Limited, Alkham Limited, Prestige Limited, da kuma Opetrus Global Limited.

A cewar Lauya Bello, an aikata laifukan ne daga tsakanin watan Janairun 2022 zuwa Disamban 2023.

Shi kuwa Ba’indiyen, wanda ke aiki da kamfanonin Regal Gate Limited, Alkham Limited, da Prestige Limited, kuma kamfanin Dangote ya ɗauke shi kwangila, ana zarginsa da karkatar da lita miliyan 1,530,893 ta dizel da aka ƙimanta farashinsa a kan naira biliyan 1.53.

Mai shigar da ƙarar ya bayyana cewa laifukan sun ci karo da dokokin Nijeriya na kundin tsarin mulki da suka haramta halatta kuɗaɗen haram.

Bello ya ce tuni aka bayar da belin wasu daga cikin waɗanda ake zargin bisa sharaɗoɗi daban-daban.

A yanzu alkalin ya ɗaga shari’ar har sai ranar 22 da 23 ga watan Yuli don ci gaba da sauraron ƙarar.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us