TURKIYYA
2 minti karatu
Erdogan ya isa Azerbaijan don halartar muhimmin taron yankin kan tattalin arziki
Shugaban Ƙasar Turkiyya na halartar Babban Taron ECO karo na 17 a yankin Karabakh na Azerbaijan, yana mai jaddada aniyar Turkiyya kan haɓaka tattalin arziki da siyasar yankin.
Erdogan ya isa Azerbaijan don halartar muhimmin taron yankin kan tattalin arziki
Turkiyya babbar kawa ce ga Azerbaijan, kuma ta taimaka wa Baku wajen ciyar da kasar gaba bayan gwabza yaki (Photo: AA) / AA
4 Yuli 2025

Shugaban Ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya isa Azerbaijan don halartar Babban Taron Ƙungiyar Haɗin Kan Tallin Arziki (ECO) karo na 17, taron yankin mai muhimmanci da ke manufar haɓaka tattalin arzikin ƙasashe mambobin ƙungiyar.

Ana gudanar da taron a garin Khankendi da ke yankin Karabak.

Shugaban na Turkiyya ya samu rakiyar manyan jami’ai da suka haɗa da Ministan Harkokin Wajen Hakan Fidan, Ministan Kasuwanci Omer Bolat, Ministan Sufuri da Gina Ƙasa Abdulkadir Uraloglu, da Ministar Iyali da Hidimtawa Al’umma Mahinur Ozdemir Goktas.

Ana sa ran shugaba Erdogan zai gabatar da jawabi a wajen taron, inda shugabanni daga ƙasashe goma mambobin ECO za su tattauna kan karfafa hadin kan kasuwanci, makamashi, sufuri, da sauran fannoni masu muhimmanci.

Ƙungiya mai muhimmanci

An kafa ECO a 1985 da mambobi uku na Turkiyya, Iran da Pakistan, inda a yanzu ta kara girmama da mamboni daga Tsakiyar Asiya da Kudancin Caucasia bayan rushewar Tarayyar Soviet.

Taron nata na zama wani dandali na habaka haɗin kan tattalin arziki, cuɗanya tsakanin ƙasashen yankin, da tattaunawar siyasa.

Taron na wannan shekarar na zuwa ne a lokacin da aka mayar da hankali kan Kudancin Caucasia, musamman bayan da Azerbaijan ta karbe iko da Karabakh bayan rikicin da ta fafata da Armenia.

Turkiyya babbar kawa ce ga Azerbaijan, kuma ta taimaka wa Baku wajen ciyar da kasar gaba bayan gwabza yaki ta hanyar fadada hanyoyin sufuri zuwa Asiya da Turai, ciki har da babban aikin Hanyar Tsakiya.

Halartar Erdogan taron na bayyana aniyar Ankara wajen cin gaba da hadin kai a yankin da zurfafa dangantaka da Azerbaijan.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us