NIJERIYA
2 minti karatu
Dakarun Nijeriya sun harbe ƙasurgumin ɗan ta’adda a dajin Borno
Rahotanni sun ce an daɗe ana neman Abu Fatima ruwa-a-jallo inda aka yi alƙawarin bai wa duk wanda ya gano inda yake naira miliyan 100.
Dakarun Nijeriya sun harbe ƙasurgumin ɗan ta’adda a dajin Borno
hare-haren 'yan Boko Haram kan sojojin Nijeriya sun fara ƙaruwa cikin 'yan makonnin nan / AP
30 Mayu 2025

Dakaru na musamman na rundunar Operation HADIN KAI da ke yaƙi da ‘yan ta’adda a arewa maso gabashin Nijeriya sun kashe wani ƙasurgumin kwamandan ‘yan Boko Haram, , Amir Abu Fatima, a jihar Borno.

Wata sanarwa da rundunar sojin Nijeriya ta wallafa a shafinta na X ta ce sojojin sun kashe Abu Fatima da wasu ‘yan ta’adda ne kusa da Kukawa a jihar Borno.

Baya ga sanarwar sojin, wasu rahotanni a Nijeriyar suna nuna cewa rundunar sojin ta samu nasarar kashe kwamadan na Boko Haram ne bayan ta kai wani farmaki na musamman domin kawar da manyan ‘yan ta’adda da sanyin safaiyar ranar juma’a.

Zagazola Makama da ke watsa labarai kan lamuran tsaro a yankin, ya ruwato cewa dakaru na musamman sun yi nasarar kama Abu Fatima din bayan ya ji rauni a lokacin da suka yi musayar wuta da shi da ‘yan ta’addan da ke tare da shi a daji.

Sai dai kuma ya rasa ransa saboda yawan jinin da ya rasa bayan ya ji ciwo a bata-kashin da sojoji suka yi da mayaƙan na Boko Haram.

Rahoton ya ƙara da cewa an kashe mataimakinsa da masu haɗa bam da sauran wasu mayaƙan a lokacin musayar wutan inda sojoji suka ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 da kayayyakin haɗa bam.

Rahotanni sun ce an daɗe ana neman Abu Fatima ruwa-a-jallo inda aka yi alƙawarin bai wa duk wanda ya gano inda yake naira miliyan 100.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us