SIYASA
3 minti karatu
Turkiyya ta jaddada goyon bayanta ga Syria a wajen taron haɗin kai a Damascus
Altun ya ce Turkiyya na goyon bayan Syria domin ta samar da makomarta tare da ƙarfafa alaƙarsu da haɗin kai a dukkan ɓangarori.
Turkiyya ta jaddada goyon bayanta ga Syria a wajen taron haɗin kai a Damascus
Taron ya tattara malaman jami’a, ’yan jarida, kungiyoyi masu zaman kansu, jami’ai, da kuma mahalarta na kasa da kasa. / AA
9 Yuli 2025

Shugaban Sashen Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya bayyana aniyar Ankara ga zaman lafiya da walwalar jama’ar Syria, yana mai jaddada cewa alaƙar ƙasashen biyu ta wuce batun maƙotaka, ta shafi daɗaɗɗiyar dangantar al’adu, tarihi da addini.

A saƙon da ya fitar a wajen wani zaman tattaunawa mai taken “Haɗin Kai bisa Hanyar Zaman Lafiya da Kwanciyar Hankali: ‘Yan’Uwantakar Turkiyya da Syria” da aka gudanar a Damascus a ranar Talata, Altun ya ce wannan kyakkyawar alaƙa ta ci gaba har a lokuta masu wahala, zamanin mulkin Baath, wanda ya ce ya janyo ‘wahalhalu 'masu yawa’ ga jama’ar Syria.

“Mulkin Baath da ya janyo mutuwar dubban ‘yan ƙasar Syria kuma ɗaya daga cikin rikicin jinƙai mafiya muni a tarhin baya bayan nan, madalla ya zo ƙarshe,” in ji Altun.

“Na yi amanna jama’ar Syria na tafiya a turbar cigaba, mai zaman lafiya da makomai mai kyau.”

Ya jaddada matakin Turkiyya na kasance wa tare da waɗanda ake zalunta a tarihi, musamman a shekaru mafi wahala ga ‘yan Syria, yana mai yaba wa Shugaban Ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan saboda taimaka wa ‘yan Syria.

Altun ya bayyana cikakken taimakon da Turkiyya ta bayar a lokacin rikicin, daga agajin jinƙai zuwa kiwon lafiya, ilimi da tallafin jin daɗin rayuwa ga 'yan Syria da suka rasa matsugunansu, dukka a cikin Turkiyya da kan iyakokinsu. Cibiyoyin da suka haɗa da AFAD, Red Crescent da TIKA sun taka muhimmiyar rawa, in ji Altun.

Girmamar haɗin kai a ɓangarori da dama

Da yake jaddada goyon bayan Turkiyya ga Syria mai 'yancin samar da makomarta, Altun ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin zurfafa haɗin gwiwa a dukkan fannoni.

"Bayan sake bude ofishin jakadancinmu a Damascus, ofishin jakadancinmu a Aleppo ya fara aiki a yanzu haka, kamfanin jiragen saman Turkiyya ya dawo da zirga-zirga zuwa babban birnin Syria," in ji shi, ya ƙara da cewa ziyarar da ƙasashen biyu ke yi da haɗin gwiwa a harkokin sufurin jiragen sama, kasuwanci, kiwon lafiya da makamashi na ƙara samun tagomashi.

Altun ya kuma jaddada muhimmancin kokarin haɗin gwiwa a kafofin yaɗa labarai, sadarwa, diflomasiyyar jama'a da yaƙi da yada labaran ƙarya, tare da lura da kusantar ma'aikatar yaɗa labarai ta Syria. Ya bayyana ƙwarin gwiwar cewa zaman tattaunawar zai taimaka wajen ƙarfafa alaka tsakanin ƙasashen biyu.

Taron ya tattara malaman jami’a, ’yan jarida, ƙungiyoyi masu zaman kansu, jami’ai, da kuma mahalarta na ƙasa da ƙasa.

Tattaunawar ta mayar da hankali kan makomar haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu a muhimman fannoni kamar kafofin watsa labarai, sadarwa da sake gina haɗin gwiwar zaman tare a ƙasar Syria.

Taron ya kammalu da nuna wani shiri mai taken "Rikicin Syria: Diflomasiyyar Zaman Lafiya ta Turkiyya", wanda Hukumar Sadarwa ta Turkiyya ta shirya.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us