A lokacin da Cheikh Sabaly ya zura ƙwallo na uku a tawagar Senegal a ragar Ingila a filin wasan City Ground ranar Talata, ya taimaka wa ƙasar ta yammacin Afirka wajen kafa tarihin kasancewa ƙasar Afirka ta farko da ta fara doke Ingila a wasan ƙwallon ƙafa.
Tawagar ta Teranga Lions ta koci Pape Thiaw ta yi nasarar doke Ingila da ci 3-1 – inda ta zama tawagar wata ƙasar Afirka ta farko da ta doke tawagar Three Lions ta Ingila cikin wasannin 22 ƙasashen Afirka suka yi da Ingila.
Ismaila Sarr da Habib Diarra ne suka fara wa zura wa Senegal ƙwallo a ragar Ingila bayan tawagar ta Harry Kane da Thomas Tuchel ta kasance a kan gaba da farkon wasan na sada zumunci.
Senegal ba ta sha kaye a wasa ko ɗaya ba tun watan Janairun shekarar 2024, lokacin da Ivory Coast ta doke ta a bugun fenareti a matakin bugun sili ɗaya ƙwale na Gasar AFCON.
A watan Disamba ne dai Thiaw ya karɓi ragamar tawagar, kuma daga wancan lokacin tawagar ta yi nasara a wasanni biyu tare da canjaras a wasanni biyu.
Huɗu daga cikin ‘yan wasan Senegal da aka fara wasan da su a filin wasan na City Ground suna taka leda ne a Gasar Firimiya, inda Edouard Mendy da Koulibaly suka taɓa buga wa Chelsea ƙwallo a baya.
A cikin wasanni 21 da Ingila ta yi a baya da ƙasashen Afirka, tawagar Three Lions ta yi nasara a wasanni 15 kuma ta yi canjaras a wasanni shida, in ji Opta, kamfanin Birtaniya mai ba da ƙididdiga kan wasanni.
Saura ƙiris tawagar ta sha kaye a hannun Tunisiya a shekarar 1990, kafin Steve Bull ya ceto ta a wasan da aka ƙare kunnen doki inda ya zura ƙwallo ragar Tunisiya a minti 89 da fara wasa a wasan sada zumuntan da suka yi gabannin Gasar Cin Kofin Duniya.
Ingila ta sha gaban Kamaru cikin ƙarin lokaci a Gasar Cin Kofin Duniya ta Italiya 1990, inda ta fitar da su daga gasar da ci 3-2 a matakin kusa da daf da na ƙarshe
Lokaci na baya bayan nan da Ingila ta sha kaye a hannun wata tawaga daga wata nahiya shi ne shekarar 2003, lokacin da ƙasar Austireliya ta doke ta da ci 3-1 a filin wasan Upton Park.