Turkiyya za ta karɓi baƙuncin taron shugabannin NATO na shekarar 2026 a babban birnin kasar, Ankara, kuma za a shirya wajen da za a ɗauki muhimman matakai, in ji shugaban Turkiyya.
A cikin jawabin da ya yi bayan taron majalisar zartarwa a Ankara a ranar Litinin, Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa suna farin ciki da ci-gaban da aka samu cikin kanƙanin lokaci a matsayin wani ɓangare na matakin kawar da ta'addanci daga Turkiyya.
"Akwai alamun cewa wasu ɓangarori a cikin kasarmu da kuma a cikin (kungiyar ta'addanci ta PKK) suna ƙoƙarin yin zagon ƙasa don lalata ci-gaban da ake samu. ƙasarmu ba za ta faɗa tarkon su ba," in ji Erdogan.
"Abubuwan da suka faru kwanan nan a yankinmu sun tabbatar da yadda wannan matakin ya kasance kai-da-kai kuma tsararre," in ji Erdogan.
An rusa ƙungiyar ta'addanci
Kungiyar ta'addanci ta PKK, wadda ta kasance sanadiyyar zubar da jini da tashin hankali shekaru masu tawa, ta sanar da rushe kanta da kuma ajiye makamai bayan wani taro da aka gudanar daga ranar 5 zuwa 7 ga watan Mayu a arewacin Iraƙi.
Kungiyar ta'addanci ta PKK ta daɗe tana zama babbar barazana ga tsaron ƙasa da kuma zaman lafiyar yankin.
Ankara ta sha jaddada cewa babu wani wuri da ya dace da kungiyar ta'addanci a ciki ko kusa da iyakokin Turkiyya, kuma abin da ya dace kawai shi ne kawar da duk wani aiki na ta'addanci ta hanyar ajiye makamai ba tare da sharaɗi ba da kuma rushe ƙungiyoyin.
Turkiyya, da EU, da Amurka, da NATO, da kuma wasu ƙasashe da dama a duniya sun amince cewa PKK ƙungiyar ta'addanci ce. A cikin shekaru fiye da 40, ƙungiyar ta ta'addanci ta yi sanadin mutuwar dubban yara, da mata da maza.