TURKIYYA
4 minti karatu
Erdogan ya yi ganawa da dama da manyan shugabanni a wajen taron NATO
A ganawar da ya yi, shugaban Turkiyya ya yi maraba da tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Iran, ya jaddada buƙatar zaman lafiya mai ɗorewa, da gaggawar samar da dawwamammiyar tsagaita wuta a Gaza a yayin da al’amura ke rincaɓewa.
Erdogan ya yi ganawa da dama da manyan shugabanni a wajen taron NATO
Shugaba Erdogan da Merz / AA
25 Yuni 2025

Shugaban Turkiyya recep Tayyip Erdogan na yin muhimman ganawa a jejjeere a wajen Taron Shugabannin NATO a birnin Hague, inada yake gabatar da batutuwan ƙasa da ƙasa da na ƙarfafa alaƙa da manyan ƙawaye.

Taron ya kuma shaida sanarwar cewa Turkiyya ce za ta karɓi baƙuncin Taron NATO a 2026, wanda babban abu ne ga rawar da ƙasar ke taka wa a ƙawancen.

Birtaniya

Erdogan ya gana da Firaministan Birtaniya Keir Starmer, inda shugabannin biyu suka tattauna kan inganta haɗin gwiwa tsakanin Turkiyya da Birtaniya. Yayin da yake jaddada manufa ɗaya ta bunƙasa kasuwancin ƙasashen biyu zuwa dala biliyan 30, Erdogan ya bayyana yadda ake samun ƙaruwar haɗin gwiwa da aiki tare a ɓangaren tsaro.

Ya nanata aniyar Turkiyya ta tallafa wa ƙoƙarin samar da zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine, ya kuma bayyana damuwarsa kan mummunan halin jin ƙai a Gaza, inda ya yi kira da a tsagaita buɗe wuta da kuma kare dokokin ƙasa da ƙasa a Falasɗinu.

Ya kuma bayyana fatansa na ganin Iran da Isra'ila za su ci gaba da aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta, yana mai jaddada cewa, bai kamata a bar tashin hankalin ya mamaye mummunan halin jin ƙai a Gaza ba.

Ya kuma jaddada cewa, keta dokokin ƙasa da ƙasa da gwamnatin Netanyahu ke yi a Falasɗinu abu ne da ba za a amince da shi ba, kuma abin da Turkiyya ta sa gaba shi ne samar da tsagaita wuta mai ɗorewa a Gaza da kuma kai kayan agaji ba tare da kawo cikas ba.

Erdogan ya kuma yi gargaɗin cewa hare-haren da Isra'ila ke kai wa Siriya na iya dagula zaman lafiya a yankin, inda ya kuma jaddada goyon bayan Turkiyya ga kasar Siriya mai haɗin kan siyasa don bayar da damar komawar 'yan gudun hijira lafiya.

Faransa

A ganawar da ya yi da shugaban Faransa Emmanuel Macron, Shugaba Erdogan ya jaddada buƙatar mayar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Iran zuwa kwanciyar hankali na dogon lokaci.

Shugabannin sun tattauna kan yadda za'a ƙarfafa alaƙar Turkiyya da Faransa tare da yin musayar ra'ayi kan harkokin tsaro a nahiyar Turai.

Ya yi nuni da cewa, sabon tsarin tsaro da zai haɗa da ƙasashen da ba na Turai ba, zai kasance mai fa'ida tare da jaddada muhimmancin tunkarar dangantakar Turkiyya da Tarayyar Turai ta mahanga da dabaru na dogon lokaci.

Ya kuma buƙaci da a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza, yana mai yin la'akari da yadda matsalar jin ƙai ke ƙara ta'azzara.

Erdogan ya kuma bayyana cewa, Syria na taka tsan-tsan wajen kasancewa ba a cikin rigingimun yankin ba, sannan ya jaddada muhimmancin Isra'ila ta fahimci cewa tabbatar da tsaron kanta ya dogara ne kan zaman lafiyar maƙwabtanta.

Jamus

A tattaunawar sa da shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz, Shugaba Erdogan ya tabbatar da kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Turkiyya da Jamus. Ya bayyana fatan faɗaɗa haɗin gwiwa a fannonin ciniki, da makamashi, da tsaro a sabon lokacin da ake shiga.

Shugaban ya nanata aniyar Turkiyya ta zurfafa alaƙarta da Tarayyar Turai, sannan ya yi kira da a samar da irin wannan tsari mai inganci daga Tarayyar.

Dangane da batutuwan da suka shafi yankin, Erdogan ya jaddada buƙatar samar da zaman lafiya na adalci a Ukraine da kuma kwanciyar hankali mai ɗorewa tsakanin Isra'ila da Iran. Ya kuma yi nuni da yadda rikicin jin ƙai ke ƙara taɓarɓarewa a Gaza tare da jaddada cewa inganta yanayin zamantakewa da tattalin arziki a Siriya na da matukar muhimmanci don bayar da damar komawar 'yan gudun hijira zuwa gida.

A nasa ɓangaren, Shugaban Gwamnatin Jamus Merz, ya yaba da ƙoƙarin diflomasiyya da Turkiyya ke yi, musamman rawar da ta taka wajen shiga tsakani don yuwuwar ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta da samar da zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine.

Merz ya ce "Na gode masa saboda yadda Turkiyya ta nuna aniyar ɗaukar nauyin shiga tsakani, ciki har da bayar da Istanbul ko Ankara a matsayin wuraren gudanar da irin wannan taro." "Na kuma nemi Shugaba Erdogan da ya yi amfani da tasirinsa kan Rasha da shugaban Rasha da ya zo su zauna a teburin tattaunawa ta yadda, bayan wannan mummunan yaƙin na shekaru uku da rabi a Ukraine, a ƙarshe a iya samar da zaman lafiya."

Holland

Shugaba Erdogan ya kuma tattauna da Firaministan Holland Dick Schoof, inda ya kuma ci gaba da tattaunawa da manyan shugabanni a yayin taron. Ganawar tasu ta taɓo alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu da kuma ci-gaban yankin, a matsayin wani ɓangare na manyan manufofin diflomasiyya na Turkiyya.

Romania

Erdogan ya kuma tattauna da Shugaban Romania Nicusor Dan a yayin taron na awancen tsaro na NATO, inda shugabannin biyu suka tattauna kan alakar kasashen biyu.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us