SIYASA
2 minti karatu
Turkiyya ta ƙarfafa tsaron iyakokinta saboda taɓarɓarewar rikicin Isra’ila da Iran
Ministan Tsaron Turkiyya ya soki hare-haren Isra’ila da ba sa kan ka’ida, ya kuma bayyana dabarunsu na kare kasar da garkuwar makamai masu linzami ta “Steel Dome” (Kubbar Karfe).
Turkiyya ta ƙarfafa tsaron iyakokinta saboda taɓarɓarewar rikicin Isra’ila da Iran
Ministan Tsaron kasar Yasar Guler / AA
18 Yuni 2025

Turkiyya ta karfafa tsaron kan iyakokinta da na sararin samaniya saboda tabarbarewar rikici a Gabas ta Tsakiya, a yayin da Ministan Tsaron kasar Yasar Guler ya soki hare-haren da Irsa’ila take kai wa Iran, kuma ya yi gargadi kan rikita yankin.

A yayin ganawar bidiyo da kwamandoji a ranar Laraba, Guler, ya jaddada cewa Turkiyya na bin diddigin halin da ake ciki tun bayan fara kai harin, inda take daukar ‘muhimman matakan’ tsare iyakokinta.

“Bisa umarnin shugaban ƙasa, muna aiki ne da matakan riga-kafi,” in ji shi. “Ta hanyar aiki da cibiyoyinmu, muna duba dukkan hali da yanayin da ka iya shafar kasarmu.”

“Muna sukar hare-hare da ba sa bisa ka’ida na Isra’ila kan Iran, makociyarmu, a ranar Juma’ar makon da ya gabata,” Guler ya fada.

“Ayyukan sojin Isra’ila da ba halastattu ba - da farko a Gaza, sannan Lebanon, a yanzu kuma Iran - na sake bayyana ƙarara niyyarta ta yaɗa rikici a dukkan yankin.”

“Isra’ila na jan yankinmu zuwa rikici,“ i ji shi, yana mai kira ga ƙasashen duniya da su ɗauki matakan dakatar da Isra’ila daga matakinta na kawo hatsaniya a yankin.”

Garkuwar makamai masu linzami ta 'Steel Dome' (Kubbar Karfe)

Ministan tsaron ya kuma bayyana dabarun tsaron Turkiyya na dogon zango, ciki har da samar da garkuwar makamai masu linzami da aka baiwa sunan ‘Steel Dome’ (Ƙubbar Karfe).

Ana sa ran garkuwar za ta yi aiki da jirgin yaki na Kaan da aka samar a cikin ƙasar da kuma wasu makamai masu linzami.

“A karkashin jagorancin shugabanmu, babbar manufarmu ita ce mu samu tsaro mai ƙarfi don kare kasarmu ta hanyar amfani da ‘Kubbar Karfe’,” in ji Guler.

Ya ƙarkare da tabbatar da matakin Turkiyya na ba za ta tsaya kawai tana sanya idanu kan abubuwan da ke afkuwa a yankin ba.

“Za mu ci gaba da ɗabbaka manyan manufofinmu na tsaro da kariya sosai, ta hanyar ɗaukar matakan da suka kamata ba tare da sassautawa ba.”

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us