NIJERIYA
2 minti karatu
Gwamnatin Filato ta bai wa masu babura wa'adin sa'a 72 su daina yawo a cikin Jos da Bukuru
Hukumomin kasar sun bayyana cewa sama da babura 400 ne suka mamaye yankin a ‘yan kwanakin nan, wanda hakan ya sabawa tsarin babban birnin Jos, wanda ya haramta amfani da babur a cikin birnin
Gwamnatin Filato ta bai wa masu babura wa'adin sa'a 72 su daina yawo a cikin Jos da Bukuru
Gwamnati Filato ta jaddada cewa wannan shi ne karo na ƙarshe da za ta kara irin wannan gargadi. / TRT Afrika Hausa
3 Yuni 2025

Gwamnatin Jihar Filato da ke yankin arewa maso tsakiyar Nijeriya ta yi gargadi bisa karuwar babura da ke aiki ba bisa ka’ida ba a cikin babban birnin Jos-Bukuru, lamarin da ya sa ta baiwa masu babura wa’adin sao’i 72 kan bar wuraren da aka takaita zirga-zirgansu.

Hukumomin kasar sun bayyana cewa sama da babura 400 ne suka mamaye yankin a ‘yan kwanakin nan, wanda hakan ya sabawa tsarin babban birnin Jos, wanda ya haramta amfani da babur a cikin birnin.

A wata sanarwa da Hon. Davou Jatau Gyang, kwamishinan sufuri ya fitar ya ce, gwamnati ta jaddada cewa wannan shi ne karo na ƙarshe da za ta kara irin wannan gargadi.

"Mun ƙuduri aniyar tabbatar da tsaron jama'a, da aiwatar da doka, da kuma tabbatar da zaman lafiya. Masu amfani da babura da suka ki bin doka za su fuskanci hukunci mai tsauri," i.n ji Gyang

Don tabbatar da an bi cikakken bin doka, an baza kotunan tafi da gidanka a duk fadin Jos-Bukuru, wadanda suke shirye su gurfanar da duk wani mai laifi da ke aiki a yankunan da aka takaita zirga-zirgan.

Kazalika gwamnatin jihar ta jaddada cewa, babu sausauci a matakin da ta dauka na haramcin babur, kuma hakan wani bangare ne na kokarin da ake yi na magance cunkoson ababen hawa a birane, da rage hadurran da ke shafar babura da kuma magance matsalolin tsaro.

Ta kuma yi kira ga mazauna yankin da su ba da goyon baya ga kokarin tabbatar da tsaro, yayin da ake tunatar da masu aiki da su mutunta doka don kauce wa rikici da hukumomi.

"Mun fahimci mahimmancin babura a harkokin sufuri, amma kiyaye lafiyar jama'a da bin doka ya zama dole," in ji Kwamishinan.

.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us