13 Mayu 2025
Kungiyar kasashen kawance ta AES wadda ta hada Mali da Burkina Fasa da Nijar ta gabatar da sabuwar take na Kungiyar ta La Confederale a hukumance ga shugaban kasar Mali Assimi Goita a ranar Litinin.
Ministocin al'adu na kasashen uku ne suka jagoranci kaddamar da bikin taken a Bamako, inda suka bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki na karfafa kungiyar.
Taken wakar wadda mutane 15 suka rera na nuna irin sadaukarwar da ƙungiyar kasashen uku suka yi wajen samar da haɗin kai da yancin kai a yanayin tarin ƙalubalen da yankin ke fama da su.