NIJERIYA
2 minti karatu
Rikicin Benue: Shugaba Tinubu zai kai ziyara jihar
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya dage ziyarar da ya shirya kaiwa jihar Kaduna. Maimakon haka zai fara zuwa jihar Benue a ranar Laraba, 18 ga Yuni don nemo bakin zaren rikicin da ake fama da shi a jihar, cewar kakakinsa Bayo Onanuga.
Rikicin Benue: Shugaba Tinubu zai kai ziyara jihar
A 'yan watannin nan jihar Benue da ke areea ta tsakiyar Nijeriya na fama da hare-hare inda ake samun asarar rayuka. / TRT Afrika Hausa / Reuters
16 Yuni 2025

An dage ziyarar da shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya shirya kai wa jihar Kaduna, inda zai fara ziyartar Jihar Benue da ke fama da rikice-rikicen da suka janyo asarar rayuka da dukiyoyi.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Nijeriya, Bayo Onanuga ya fitar ta shafin X a ranar Litinin, an bayyana cewa ziyarar na da manufar yin duban tsanaki da neman mafita ga rikicin da ya yi ajalin mutane da dama a Benue.

Sanarwar ta ce a yayin ziyarar, Tinubu zai gana da dukkan masu ruwa da tsaki, - ciki har da shugabannin gargajiya, ‘yan siyasa, shugabannin addini, shugabannin jama’a, da kungiyoyin matasa - don lalubo bakin zaren rikicin da ake samu a jihar da ke yankin tsakiyar Nijeriya.

“A shirye-shiryen ziyarar, tuni shugaba Tinubu ya tura Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sufetan ‘Yan Sanda, da shugabannin hukumomin leken asiri, da Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro, da Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dattawa zuwa Jihar Benue,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa a baya shugaba Tinubu ya soki irin hare-haren da ake kai wa a Jihar Benue, inda ya yi kira ga shugabanni da mazauna yankin da su rungumi zaman lafiya, kauna, da fahimtar juna. Ya kuma mika sakon ta’aziyya da jaje ga iyalan wadanda rikice-rikicen suka rutsa da su.

Tun da fari, bayanan ayyukan da shugaban na Nijeriya zai yi a makon nan sun bayyana cewa zai kai ziyarar aiki zuwa Jihar Kaduna a ranar Laraba, tare da kaddamar da wasu ayyukan gwamnatin jihar.

An dage ziyarar shugaban zuwa Kaduna har sai ranar Alhamis, 19 ga Yunin 2025.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us