Shahararren mai tsaron ragar tawagar Nijeriya ta Super Eagles, Peter Rufai ya rasu yana da shekaru 61.
'Yan Nijeriya sun shiga jimamin rashin wannan gwarzo, wanda ya rasu ranar Alhamis bayan wata rashin lafiya da ba a bayyana nau’inta ba.
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta bayyana Peter Rufai a matsayin gwarzon ƙwallon kafa.
Sanarwar NFF ta ce, "Zai kasance har abada a zukatanmu, Dodo Mayana. Muna jimamin rasuwar shahararren mai tsaron ragar Super Eagles, Peter Rufai, gwarzon ƙwallon ƙafa na Nijeriya kuma zakaran AFCON na 1994.”
“Tarihin da ka bari zai ci gaba da kasancewa a ragarmu da kuma sauran wurare," in ji sanarwar.
An haifi Peter Rufai ranar 27 ga Agusta, 1963 a Legas. Ya wakilci tawagar ƙwallon Nijeriya, Super Eagles, tsawon kusan shekaru ashirin.
Ya buga mata wasanni 65, inda ya nuna ƙwarewa, da kwarjini, da hanzari, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar Super Eagles a gasar cin kofin Afrika na 1994 a Tunisia, bayan sun kasance na biyu a shekarun 1984 da 1988.
Wasa a Turai
Peter Rufai ya buga wa Nijeriya a gasar cin kofin duniya ta USA 1994 da France 1998, bayan ya fara buga wasa na ƙasa tun a Disamban 1981.
Gudunmawarsa ga ƙwallon ƙafa a Nijeriya ta bar tarihi mai tsawo, kuma yana ci gaba da zama abin koyi ga matasan 'yan wasa masu tasowa.
Tsohon abokin wasansa, Kanu Nwankwo, ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan Peter Rufai, yana bayyana shi a matsayin gwarzon Afrika.
"Yau rana mai duhu ce a ƙwallon ƙafa. Mun rasa gwarzon Afrika Peter Rufai. Allah ya jikansa da rahama. Amin." in ji Kanu a shafinsa na X.
Peter Rufai ya taka leda a ƙungiyoyi daban-daban a Turai, ciki har da a Belgium tare da K.S.C. Lokeren Oost-Vlaanderen, da K.S.K. Beveren, da kuma a Netherlands tare da Go Ahead Eagles, da Portugal, tare da S.C. Farense da Gil Vicente FC, da kuma a Spain tare da Hércules CF da Deportivo La Coruña..