NIJERIYA
2 minti karatu
Sojojin Nijeriya sun kashe gomman ‘yan Boko Haram a Tafkin Chadi
A makonnin baya bayan nan dai hare-haren ‘yan Boko Haram suna ƙoƙarin dawowa arewa maso gabashin Nijeriya.
Sojojin Nijeriya sun kashe gomman ‘yan Boko Haram a Tafkin Chadi
Boko Haram, wadda ke kai hare-hare a Nijeriya tun daga shekarar 2009, ta yi sanadin mutuwar dubban mutane da raba miliyoyi da muhallansu. / Nigerian army
18 Yuni 2025

Rundunar sojin Nijeriya ta yi shelar kashe gomman ‘yan ta’adda na ISWAP/Boko Haram da suka yi ƙoƙarin kutsawa cikin sansanin sojin ruwan ƙasar a yankin Tafkin Chadi.

Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X ranar Laraba ta ce ‘yan ta’addan sun yi ƙoƙarin kutsawa cikin sansanin sojojin ne da misalin ƙarfe 2 na dare inda suka yi ƙoƙarin lalata sabbin motocin tafiya a fadama waɗanda gwamnatin Jihar Borno ta saya domin yashe hanyoyin ruwa.

  Sai dai jami’ai a sansanin sojin ruwan Nijeriya da ke Tafkin Chadin sun jajirce wajen hana su kutsawa inda aka yi ta musayar wuta har tsawon sama da sa’o’i biyu inda aka kai musu  ɗauki daga Baga kana ‘yan ta’addan suka ja da baya ba tare da sun kai ga motocin tafiya cikin fadamar ba, in ji sanarwar.

Baya ga kashe gomman ‘yan ta’addan, sanarwar ta ce sojojin sun yi nasarar kwato ababe masu fashewa yayi da wasu daga cikin jam’ian tsaron suka ji rauni.

“Ɓangaren sojin sama [na rundunar] na bin sawun [‘yan ta’addan] a kan ruwa domin ƙara kassara su,” in ji sanarwar.

A makonnin baya bayan nan dai hare-haren ‘yan Boko Haram suna ƙoƙarin dawowa arewa maso gabashin Nijeriya.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us