NIJERIYA
1 minti karatu
Fitaccen attajirin Nijeriya Aminu Alhassan Dantata ya rasu
Dantata ya rasu ne a safiyar Asabar a birnin Abu Dhabi na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, a cewar ɗaya daga cikin makusantansa Sanusi Dantata.
Fitaccen attajirin Nijeriya Aminu Alhassan Dantata ya rasu
Aminu Dantata, ɗan uwa ne ga shahararren mai kuɗin nan na Afirka Alhaji Aliko Dangote / Others
28 Yuni 2025

Hamshaƙin attajirin nan na Nijeriya Alhaji Aminu Alhassan Dantata ya rasu yana da shekara 94.

Dantata ya rasu ne a safiyar Asabar a birnin Abu Dhabi na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, a cewar ɗaya daga cikin makusantansa Sanusi Dantata.

Alhaji Aminu ne ɗa na ƙarshe wanda ke da rai a cikin ‘ya’yan Alhassan Dantata kafin rasuwarsa a ranar Asabar.

Ya yi fice wurin kasuwanci da kuma taimakon al’umma. A shekarar da ta gabata, ya bayar da kyautar naira biliyan 1.5 ga iyalan waɗanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Jihar Borno.

Aminu Dantata, ɗan uwa ne ga shahararren mai kuɗin nan na Afirka Alhaji Aliko Dangote.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us