NIJERIYA
2 minti karatu
Lakurawa sun kashe sojojin Nijeriya biyar a Sokoto
Lamarin ya faru ne a lokacin da sojojin ke ƙoƙarin fatattakar Lakurawan inda sojojin suka samu kashe shida daga cikin 'yan ta'addan.
Lakurawa sun kashe sojojin Nijeriya biyar a Sokoto
Ƙungiyar Lakurawa ta yi ƙaurin suna ne a ƙarshen shekarar 2024. / Hoto: NA / User Upload
17 Janairu 2025

Rundunar Sojin Nijeriya ta tabbatar da mutuwar sojojinta biyar a yayin wata arangama da suka yi da ‘yan ta’addan Lakurawa a Jihar Sokoto.

Lamarin ya faru ne a lokacin da sojoji na musamman daga hedkwatar tsaron ƙasar ke aikin fatattakar Lakurawan a Ƙaramar Hukumar Gudu da ke Jihar Sokoto.

A sanarwar da mai magana da yawun Operation Fansan Yamma Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, sojojin sun samu nasarar kashe Lakurawan shida sai dai kuma su ma a ɓangaren sojin sun yi rashin dakarunsu biyar.

Read More

Ana zargin Lakurawa da kashe ma’aikatan Airtel uku a Nijeriya

“Dakarun sun ƙwato waɗannan kayayyakin a yayin samamen, bindigar AK-47 huɗu, harsasai 160 samfurin 7.62mm, da kuma kwali guda na harsasan 12.7mm.

“Duk da wannan nasarar, amma samamen ya zo da babban ƙalubale, sakamakon jajirtattun sojoji biyar da suka rasu a yayin da suke aikin,” in ji sanarwar.

Tun bayan da ƙungiyar Lakurawa ta soma ƙaurin suna a bara, ta kai hare-hare da dama duk da cewa jami’an tsaron ƙasar sun bayyana cewa suna iya bakin ƙoƙarinsu wurin daƙile hare-harensu.

Ko a makon da ya gabata sai da wasu ‘yan ta’adda waɗanda ake zargin Lakurawan ne suka kashe ma’aikatan kamfanin sadarwa na Airtel uku da kuma wani mutum guda wanda ya fito daga ƙauyen Gumki a Ƙaramar Hukumar Arewa ta Jihar Kebbi.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us