NIJERIYA
2 minti karatu
Buhari ya taya Shugaban Nijeriya Tinubu murnar cika shekaru biyu a kan mulki
Buhari ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su kasance masu kyakkyawan fata kuma su kasance da ƙwarin gwiwa game da makomar kasar.
Buhari ya taya Shugaban Nijeriya Tinubu murnar cika shekaru biyu a kan mulki
Buhari da Tinubu / Others
28 Mayu 2025

Tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya taya Shugaba Bola Ahmed Tinubu murnar cikarsa shekara biyu a kan mulkin ƙasar, inda ya ce yayin da jam’iyya mai mulki da gwamnati suke murna, ya kamata a tuna wa ƙasar cewa shugabanci tafiya ce mai ɗorewa.

A sanarwar da mai taimaka masa kan watsa labarai, Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba, kwana ɗaya gabanin cika shekara biyu cif da rantsar da Tinubu, Buharin ya kuma yi kira ‘yan Nijeriya su ci gaba da bai wa gwamnatin APC goyon baya a daidai lokacin da take cika shekara biyu a kan karagar mulki, inda ya bayyana cewa sauye-sauyen da ake yi za samu samar nasara a hankali ne ba dare ɗaya ba.

Ya yi gargadin cewa sauye-sauyen da ake buƙata kada a jefa su cikin mummunan siyasar cikin gida.

Buhari ya kuma bayyana goyon bayansa ga kokarin da gwamnatin ke yi na daƙile fatara da hauhawar farashin kayayyaki, wanda a cewarsa ya fi yi wa iyalai wahala, inda ya ƙara da cewa, aikin rage radadin talauci da hauhawar farashin kayayyaki ba a abu ne da ya kamata a bar wa gwamnati kadai ba.

"Kamfanoni masu zaman kansu da dukkanmu a matsayinmu na 'yan kasa dole ne mu shiga cikin lamarin ta duk hanyoyin da za mu iya," in ji tsohon Shugaban Ƙasar.

Sannan Buhari ya bukaci ‘yan Nijeriya da su kasance masu kyakkyawan fata kuma su kasance da ƙwarin gwiwa game da makomar kasar.

A ƙarshen saƙon nasa Shugaba Buhari ya ce "Ina taya Shugaba Tinubu murnar cikarsa shekara biyu a kan mulki. Allah Ya ba shi ikon ci gaba da jagoranci cike da hikima da kulawa."

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us