Shugaban Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa ta Turkiyya (MIT), Ibrahim Kalin, ya kai ziyara lardin Hakkari da ke kudu maso gabashin ƙasar, ciki har da ƙananan hukumomin Yuksekova da Cukurca, domin gudanar da taruka masu muhimmanci kan tsaron yankin.
A cewar majiyoyin tsaro a ranar Alhamis, Kalin ya gana da Gwamnan Hakkari Ali Celik, da Kwamanda na biyu ta Rundunar Soja Janaral Levent Ergun, da kuma manyan jami'an soji da ma'aikatan gwamnati yayin ziyarar.
Tattaunawar ta mayar da hankali kan yanayin tsaro a kan iyakokin Turkiyya da ƙasashen Iraki da Iran da Siriya.
Jami'an sun duba matakan tsaro da ake da su a halin yanzu, da wuraren sansanonin dabarun tsaro masu muhimmanci a yankin, da kuma sababbin abubuwan da suka shafi yankunan kan iyaka.
Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ƙoƙarin ƙarfafa tsaron ƙasa da tabbatar da zaman lafiya a yankin kudu maso gabashin Turkiyya, wanda ya kasance muhimmin wuri wajen dabarun yaƙi da ta'addanci da kuma kula da iyakokin ƙasar.