Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, da Ministan Tsaron Kasa, Yasar Guler, za su kai ziyara Pakistan a ranar 9 ga Yuli domin karfafa dangantakar dabarun tsaro tsakanin kasashen biyu da kuma zurfafa hadin kai don zaman lafiya a yankin.
Majiyoyi daga Ma’aikatar Harkokin Wajen sun bayyana a ranar Talata cewa tawagar Turkiyya za ta gana da Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, da Mataimakin Firaminista kuma Ministan Harkokin Wajen, Ishaq Dar, da kuma Babban Hafsan Sojojin Pakistan, Field Marshal Syed Asim Munir.
Turkiyya da Pakistan suna da kyakkyawar dangantaka ta fuskar tattalin arziki, cinikayya, da tsaro.
Wannan ziyarar ta manyan jami’an gwamnati ana sa ran za ta kara inganta hadin kai a fannin tsaro da yaƙi da ta’addanci.
Ankara da Islamabad suna da muradin dabarun tsaro na bai daya wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin, musamman dangane da matsalolin da ta’addanci ke haifarwa.
Kasashen biyu sun yi magana da murya daya kan manyan kalubalen da ke fuskantar duniya Musulmi, musamman batun Falasdinawa.
Ana sa ran manyan jami’an Turkiyya da takwarorinsu na Pakistan za su duba ci gaban da aka samu tun bayan taron Majalisar Hadin Kan Dabarun Tsaro ta Babban Mataki (HLSCC) da aka gudanar a Islamabad a watan Fabrairu 2025.
Haka kuma za su tattauna shirin taron gaba da aka tsara gudanarwa a Turkiyya a 2026.
Turkiyya ce ta fara nuna goyon baya ga Islamabad tare da yin Allah wadai da hare-haren jiragen saman Indiya da suka kashe fararen hula 31 a farkon yakin kwanaki hudu tsakanin kasashen Kudancin Asiya a watan Mayu.
Ankara ta ci gaba da jaddada kudurinta na tallafa wa zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Ana sa ran Tawagar Turkiyya za ta tattauna matakan ƙarfafa hadin kai a fannin tsaro tsakanin kasashen biyu.
Kasashen biyu suna kallon rashin kwanciyar hankali a Afghanistan a matsayin barazana kai tsaye ga tsaron yankin.
Pakistan tana goyon bayan yakin Turkiyya da kungiyoyin ta’addanci kamar FETO, PKK, da Daesh.
Bisa ga rahoton 2023, Turkiyya ita ce ta biyu mafi girman mai samar da makamai ga Pakistan.
Ankara ta cika kashi 11 cikin 100 na bukatun makaman Islamabad a 2023 ta hanyar fitar da makamai da harsasai na kimanin dala miliyan 21.
Fidan ya kai ziyarar aiki ta farko a Pakistan daga 18 zuwa 20 ga Mayu, 2024.
Ya gana da Ministan Harkokin Wajen Pakistan, Dar, a karon karshe a Istanbul daga 21 zuwa 22 ga Yuni yayin taron ministocin harkokin wajen OIC karo na 51.
Dangantakar kasashen biyu ta samu karfi a matakin siyasa mafi girma ta hanyar kafa Majalisar Hadin Kai ta Babban Mataki a 2009, wadda daga baya aka mayar da ita Majalisar Hadin Kan Dabarun Tsaro ta Babban Mataki (HLSCC).
A karkashin wannan tsarin, tarukan HLSCC suna bayar da damar tattaunawa da inganta dangantakar kasashen biyu sosai.
Adadin cinikayya tsakanin kasashen biyu ya kai kimanin dala biliyan 1. A 2024, cinikayyar ta kai dala biliyan 1.3, inda fitar da kaya daga Turkiyya ta kai dala miliyan 918, yayin da shigo da kaya daga Pakistan ya kai dala miliyan 440.
Jimillar jarin Turkiyya a Pakistan ya kai kimanin dala biliyan 2. Kamfanonin gine-ginen Turkiyya sun gudanar da ayyuka 72 a Pakistan, da darajar jimilla ta kimanin dala biliyan 3.5.
Ana ci gaba da kokarin samar da sabbin hanyoyin hadin kai a fannonin makamashi da albarkatun kasa masu muhimmanci tsakanin kasashen biyu.
Yarjejeniyar Hada Kai ta Bidding, da aka sanya hannu a watan Afrilu 2025 tsakanin Kamfanin Man Fetur na Turkiyya da kamfanonin man fetur na kasa uku na Pakistan, tana ba da damar binciken mai da iskar gas tare, wanda ake ganin mataki ne mai muhimmanci.