WASANNI
2 minti karatu
Adam Lallana: Tsohon ɗan wasan Liverpool da Southampton ya yi ritaya daga ƙwallo
Tsohon ɗan wasan Liverpool da Southampton da Brighton, da kuma tawagar Ingila, Adam Lallana ya sanar da yin ritaya daga ƙwallon ƙafa yana da shekaru 37.
Adam Lallana: Tsohon ɗan wasan Liverpool da Southampton ya yi ritaya daga ƙwallo
/ Reuters
25 Yuni 2025

Adam Lallana, tsohon ɗan wasan Liverpool wanda ke taka leda a Southampton ya sanar da yin ritaya daga ƙwallon ƙafa a shafinsa na Instagram.

A wata sanarwa mai ratsa jiki da ya wallafa ranar Laraba, ya ce ba shi da wata nadama saboda barin ƙwallo a yanzu bayan ya kwashe shekaru 18 yana wasa a ajin ƙwararru.

Lallana, wanda ke da shekaru 37 a duniya, tsohon tauraron tawagar ƙwallo ta Ingila ne, wato Three Lions, wadda ya buga wa wasa har 34.

Adam Lallana ya koyi ƙwallon ƙafa ne a makarantar koyar da ƙwallo ta Southampton har sanda ya kai shekaru 18 a duniya a 2006.

Farawa da kammalawa a Southampton

Bayan fara ƙwallo a Southampton, Lallana ya koma Brighton da kuma Liverpool sannan ya buga wa ƙasarsa Ingila a gasar kofin duniya ta 2014. A ƙarshe ya koma Southampton inda a nan ne ya yi ritaya.

A zamansa na farko a Southampton, ya buga wasanni sama da 250 inda ya taimaka mata komawa ajin Firimiya daga ajin League One karo biyu. Ya sake komawa can bara 2024, shekarar da suka faɗo daga Firimiya.

A 2014, Lallana ya koma Liverpool kan fam miliyan £25, inda ya kwashe shekara 6 ƙarƙashin Brendan Rodgers da Jurgen Klopp a matsayin koci, inda ya lashe kofin Zakarun Turai a 2018–19 da na Firimiya a kakar 2019–20.

Da yake bayyana farin cikinsa da yadda rayuwarsa ta wasa ta kasance, Lallana ya ce "Yayin da nake kawo ƙarshen rayuwar wasana, ina hakan ne cike da gamsuwa da alfahari".

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us