TURKIYYA
2 minti karatu
Turkiyya na tunawa da waɗanda harin wutar Solingen ya rutsa da su shekaru 32 suka gabata
A shekarar 1993, an kashe ‘yan Turkiyya biyar a garin Solingen na ƙasar Jamus a lokacin da masu kaifin kishin ƙasa suka cinna wa gidansu wuta.
Turkiyya na tunawa da waɗanda harin wutar Solingen ya rutsa da su shekaru 32 suka gabata
Iyalan Genc sun rasa ‘yan gidansu biyar a lokacin da gungun masu tsassarar aƙidar Nazi huɗu suka cilla wa gidansu wuta a a garin Solingen, da ke Jamus / AA
29 Mayu 2025

Turkiyya ta tuna da waɗanda harin wariyar launin fata na shekarar 1993 ya rutsa da su a garin Solingen na Jamus inda lamarin ya kashe mutum biyar ‘yan wani iyali ɗaya ‘yan asalin Turkiyya.

"Muna tunawa tare da girmamawa ‘yan ƙasarmu biyar da suka rasa rayukansu shekaru 32 da suka wuce a harin Solingen na wariyar launin fata," kamar yadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta bayyana a wata sanarwar da ta fitar ranar Laraba.

Ma’aikatar ta kuma yaba wa Mevlude Genc, wadda ta rasa ‘ya’ya mata biyu da jikoki mata biyu da kuma ‘yar ɗan’uwanta a harin kuma daga baya ta zama wata wakiliyar sulhu a Jamus, a duk wani kira na zaman lafiya da taka tsantsan bayan aukuwar lamarin.

Ta rasu a shekarar 2022 kuma ana yawan tunawa da ita ne a matsayar “uwa mai hikima.”

"A wannan lokaci, muna sake daɗa tunawa da Mevlude Genc cikin martaba… da girmamawa da godiya," in ji ma’aikatar.

Yaƙi da wariyar launin fata da ƙin Musulunci

Sanarwar ta ƙara da cewa Turkiyya za ta ci gaba da ƙalubalantar “ƙaruwar wariyar launin fata da ƙin jinin baƙi da kuma ƙin jinin Musulunci a kowace kafa.”

A ranar 29 ga watan Mayun shekarar 1993, matasan Jamus hudu masu kaifin kishin ƙasa waɗanda shekarunsu ke tsakanin shekara 16 zuwa 23 sun cinna wuta kan gidan iyalan Genc ‘yan Turkiyya a garin Solingen, a jihar North Rhine-Westphalia.

Harin ya kashe mutum biyar tare da ji wa sauran mutum 14 rauni.

Uku daga cikin wadanda suka aikata aika-aikar an tura su gidan gyaran hali na shekara 10, inda aka yanke wa na huɗunsu hukuncin zama a gidan kaso na shekara 15.

Harin ya tayar wa Jamus hankali tare da janyo Allah wadai daga ƙasashen duniya, lamarin da ya sa aka fara muhawara game da wariyar launin fata da sajewar baƙi da al’umma a cikin ƙasar.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us