“Ba sai a watan Ramadana kawai ake iya samun burodin pide ba, in ji Ercan Bayraktar. Bayraktar, wanda shi ne mamallakin kamfanin Bayraktar Firini a Beyoglu, yana daga cikin zuriyar waɗanda suka fara gasa wannan burodi. “Amma shi piden da ake samu a Ramadan na musamman ne, irin fulawar da ake amfani da ita tana da inganci sosai,” ya ce. “Fulawar alkama ce wadda take shan ruwa sosai. Kuma tana da wani kamshi na musamman idan an gasa ta.”
Da aka tambaye shi karin bayani game da fulawar pide na Ramadan, Bayraktar ya ce masana'antar fulawa suna fara shirya wannan irin fulawa mai inganci watanni kafin Ramadan. “Yin pide na Ramadan yana nan kamar yadda yake shekaru 20 da suka wuce, ko ma lokacin yarintata,” ya kara da cewa.
Bayraktar ya ce karamin wurin yin burodi da ke cikin Balik Pazari (kasuwar kifi) a unguwar Beyoglu ta Istanbul yana nan tsawon shekaru 100 ko fiye. “Ba mu da tabbacin lokacin da aka kafa shi,” ya bayyana, “amma ya kasance shekaru da dama da suka wuce.”
Mai yin burodi Rahmi Burman a Bayraktar Firini ya ce pide na Ramadan zai manne idan ba su yi amfani da ciyawar alkama ba don raba shi daga itacen da suke amfani da shi wajen sanya pide a cikin murhun bulo.
Izzet Boz, wani ma’aikaci a wurin, ya ce pide na Ramadan yana da wani abu na musamman. Ya bayyana hakan da kalma daya: “Sifa [magani].” Abokin aikinsa Aydin Ozleyen ya kara da cewa: “Ingancin fulawa ne ke sa shi zama na musamman.”
Masaniyar tarihin abinci, Nazli Piskin, ta tabbatar da cewa a cikin Istanbul, pide ya fi yawa a lokacin Ramadan, amma ana samun sa a wasu lokutan ma. “Amma idan muka duba yankin Anatolia, ana cin pide duk shekara,” in ji ta.
“Pide wani irin burodi ne mai lebur. Muna kiran sa burodi mai lebur amma tabbas ana sa masa yis,” ta ce. “Ba kamar yufka [fulawa mai siriri da ake amfani da ita wajen yin borek], wadda ba ta da yis ba.” A cewar Piskin, fasahar mai yin pide tana bayyana ne saboda “shi pide da hannu ake mulmula shi.”
“Shi ya sa,” in ji Piskin, “kowanne wurin yin burodi yana da pide na daban.” Ta kara da cewa zafin murhu na iya bambanta daga wuri zuwa wuri, amma babban bambanci shi ne fasahar mai yin pide.
“Ana yi yin Pide da ƙwai ko ba tare da ƙwai ba,” Piskin ta bayyana. “Ba ina nufin a zuba ƙwan a cikin kwaɓin ba. Ina nufin a shafa shi a saman pide bayan an mulmula shi da hannu kafin a sanya shi a cikin murhu.”
Ta ce pide da aka gasa da ƙwai yana da launi mai ɗan rawaya zuwa ruwan kasa, yayin da wanda aka gasa ba tare da ƙai ba ya kan zama fari sosai. “Babu wani nau’i da ya fi wani,” in ji Piskin. “Kawai yana danganta ne da abin da iyali suka fi so.”
Piskin ta ce Evliya Celebi, wani matafiyi na Daular Usmaniyya a karni na 17, ya rubuta game da al’adun pide na Ramadan a Istanbul. “Ya rubuta cewa ana shafa ruwan saffron a saman pide na Ramadan kafin a gasa shi.”
Ta ce saffron zai ba da launi mai rawaya da ƙamshi mai dadi ga pide na Ramadan. Amma a yau, saffron yana da tsada sosai, don haka ba a sa ran za a yi amfani da shi.
Piskin ta ce akwai wata al’ada ta cin pide na Ramadan: “Kamar yadda kuka sani, an fi son cin pide na Ramadan da zafinsa daga wajen gasa burodin,” ta ce. “Shekaru da dama, iyalai suna tura yara zuwa wurin yin burodi don su jira a layi su sayo pide mai zafi don cin abincin buɗa-baki.”
Ta kara da cewa pide na Ramadan yana da saurin bushewa saboda yana da yawan gluten. “Ba wanda zai so cin pide mai sanyi da ya bushe,” ta bayyana. “Shi ya sa iyalai suke sayen adadin da za su iya ci kawai, don kada ya yi kwantai har washegari.”
Piskin ta ba da shawarar cewa idan ya yi kwantai, za a iya dumama shi ta hanyar turara shi a kan ruwa mai tafasa. Haka kuma, za a iya yanka shi kanana a gasa su, ko kuma a niƙa su don yin garin burodi.
Ta ce ko wane iyali yana da wurin yin burodi da suka fi so don sayen pide. “Misali, ni da mijina muna zuwa wani wurin yin burodi da ke nisan mintuna goma daga gidanmu duk da cewa akwai wani a kusa da mu wanda ba ma son saye a can,” ta bayyana.
Ta kuma ce iyalai su koya wa ‘ya’yansu tarihin Ramadan ta hanyar kai su wurin yin burodi a lokacin wata mai tsarki, ko da kuwa manyan ba sa azumi. “Wannan yana haifar da kyakkyawan tunani ga yara, kuma wata al’ada ce mai kyau,” ta kammala.