WASANNI
2 minti karatu
Thomas Partey: Ana tuhumar tsohon ɗan Arsenal kuma ɗan asalin Ghana da yin fyade
Hukumomi a Ingila sun gabatar da tuhuma biyar kan tsohon ɗan wasan Arsenal ɗan asalin Ghana bisa zargin aikata lafukan fyaɗe da cin zarafin jinsi.
Thomas Partey: Ana tuhumar tsohon ɗan Arsenal kuma ɗan asalin Ghana da yin fyade
/ Reuters
4 Yuli 2025

Wata kotu a Ingila ta tuhumi tsohon ɗan wasan Arsenal ɗan asalin Ghana da laifuka biyar masu nasaba da fyaɗe da cin zarafin jinsi.

Masu shigar da ƙara sun ce zarge-zargen sun fito ne daga wasu mata uku da suka gabatar da ƙorafin faruwar lamarin tsakanin shekarun 2021 da 2022.

A yanzu dai an tuhumi Partey da laifuka biyu ne dangane da fyaɗe kan mace ta farko, da laifuka uku na fyaɗe kan mace ta biyu, da laifi ɗaya na cin zarafin mace ta uku.

Amma sai ranar 5 ga Agusta ne Thomas Partey zai gurfana gaban kotun majistre ta Westminster kan zarge-zarge.

Bayanan da ke fitowa daga Ingila na cewa jami’an shari’a sun kammala binciken diddigi kan jerin hujjoji, ta yin aiki tare da jami’an ‘yan sanda, kafin ba da shawarar shigar da ƙarar.

Tarihin Thomas Partey

An haifi Thomas Partey a Krobo Odumase na Ghana a watan Yunin 1993, kuma ya fara wasa da Atlético Madrid ta Sifaniya a 2012, sannan ya je aro a Mallorca da Leganés.

Baya ga buga wa ƙasarsa Ghana wasanni 53 da cin ƙwallaye 15, Partey ya buga wa Atletico wasanni 188 tare da lashe kofin Europa a 2018, da La Liga a 2021.

A Oktoban 2020, Arsenal ta ɗauko Partey kan fam miliyan £45, inda ya sanya hannu kan kwantiragin shekara huɗu ƙarƙashin koci Mikel Arteta.

Thomas Partey ya yi wasa a matsayin ɗan-baya da tsakiya, inda ya buga wasanni 33 a kakarsa ta farko zuwa 2023.

Sai dai a kakar 2024 ya buga wasanni 14 ne kacal sakamakon rauni. A ƙarshe ya buga wa Arsenal jimillar wasanni 52 a duka gasanni, inda kwantiraginsa ta ƙare ran 30 ga Yunin 2025.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us