TURKIYYA
2 minti karatu
'Dabbanci, saɓa doka, abin kunya': Turkiyya ta caccaki Isra'ila bisa kai wa 'yan jarida hari
Wani babban jami'i na Turkiyya ya yi Allah wadai da Isra'ila kan hari a gidan talabijin na Iran da kuma tur da 'yan sandan Israel kan katse TRT Arabi daga watsa shirye kai-tsaye a Haifa da kuma amfani da ƙarfi kan tawagar TRT da Alghad TV.
'Dabbanci, saɓa doka, abin kunya': Turkiyya ta caccaki Isra'ila bisa kai wa 'yan jarida hari
Turkish Head of Communications calls Israeli attacks on Iranian state TV 'barbaric'. / AA
17 Yuni 2025

Daraktan Sadarwa na Turkiyya, Fahrettin Altun, ya yi Allah-wadai da matakan Isra'ila na kai hare-hare kan ma'aikatan kafafen watsa labarai, yana kiran hare-haren da sunan "dabbanci" da kuma "mummunan hari kan 'yancin 'yan jarida."

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Altun ya yi tir da harin da Isra'ila ta kai kan gidan talabijin na Iran, inda rahotanni suka ce an kashe 'yan jarida da fararen hula.

"Harin Isra'ila kan kamfanin watsa labarai na IRNA, inda aka nufi 'yan jarida da fararen hula, kisan kai ne kai-tsaye. Kai hari kan 'yan jarida da ma'aikatan kafafen watsa labarai abu ne na rashin imani," in ji shi a wani rubutu da ya wallafa a X.

Altun ya bayyana ta'aziyyarsa ga 'yan jaridar Iran da aka kashe, tare da zargin gwamnatin Isra'ila da rasa halaccinta a matsayin ƙasa saboda yadda take yi wa dokokin ƙasa da ƙasa karan tsaye.

"Muna kira ga al'ummar duniya su ɗauki mataki kan hare-haren Isra'ila da halayen rashin hankali da ke haddasa rikici a yankin," in ji shi.

‘Ayyukan da suka saɓa doka’

A wata sanarwa ta daban, Altun ya kuma soki ‘yan sandan Isra’ila da suka afka wa ɗan jaridar TRT Arabi Fahmi Shtewe da abokan aikinsa da ke tsaka da bayar da rahoto kai-tsaye a garin Haifa na arewacin ƙasar.

Ya ce an ƙwace kayan aikin ‘yan jaridar, sannan ‘yan jaridar TRT Arabi da na tashar Alghad TV ta Masar sun fuskanci cin zarafi.

“Abin takaici gwamnatin Isra’ila, na ci gaba da keta doka da oda kan ‘yan jarida da ke sanar da duniya irin kisan kiyashin da take aikata wa,” in ji Altun.

“Wannan ce shaida ta baya bayan nan ta wannan haukan.”

Da yake ƙarin haske kan abin da ya kira da shirun goyon baya na ƙasashen Yamma, Altun ya soki rashin wani martani daga cibiyoyin ƙasa da ƙasa da ke tutiyar ɗabbaka dimokuradiyya.

“Mun bar wa jama’ar duniya su yanke hukunci da kansu game da shirun da Yammacin duniya ta yi, da yadda ‘cibiyoyinsu na dimokuradiyya suke kallon waɗannan cin zarafi, musamman a lokacin da Isra’ila ce ta aikata su.”

Altun ya ƙarƙare da sake jaddada aniyar Turkiyya ta kare ‘yancin kafofin watsa labarai da haƙƙin ma’aikatan kafafen yaɗa labarai: “Za mu ci gaba da zama masu bibiya da kasancewa wani bangare na ‘yancin bayyana ra’ayi, ‘yancin samun bayanai, da hakkin ma’aikatan kafafen yaɗa labarai.”


Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us