NIJERIYA
3 minti karatu
Muna ba da fifiko wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Nijeriya – Nuhu Ribadu
Muna ba da fifiko wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Nijeriya – Nuhu Ribadu
NSA Nuhu Ribadu / Others
4 Yuni 2025

Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya ce gwamnatin tarayya na ba da fifiko wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi saboda tasirin da take da shi ga tsaron ƙasa da walwalar ‘yan kasa.

Ya alaƙanta amfani da haramtattun abubuwa—musamman a tsakanin matasa—da ƙaruwar rashin tsaro, yana mai cewa yawancin ‘yan ta’adda na amfani da miyagun ƙwayoyi.

A cewarsa, hakan na ƙara rura wutar aikata laifuka da kuma kawo cikas ga zaman lafiyar ƙasa.

Ribadu ya yi wannan magana ne a yayin wani taro da ofishinsa ya yi a Abuja da hukumomi masu ruwa da tsaki a fannin kamar hukumar hana fasa kwauri ta kasa NCS da hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ne suka gudanar da shirin.

A wajen taron, Ya bayyana shirin a matsayin shiga tsakani a fannin kiwon lafiyar jama'a na dogon lokaci tare da babban tasiri ga tsaron kasa, inda ya jaddada manufar shirin ta son raba ƙasar da abubuwa masu hadari da ke cutar da al’umma.

Ya ce gwamnati ta jajirce wajen tallafa wa ayyukan da hukumomi ke ci gaba da yi na kai hare-hare kan haramtattu da jabun magunguna.

Ya yaba da horo da hadin gwiwa da hukumomin da suka shiga suka nuna, inda ya ce nasarar aikin na nuna irin abubuwan da cibiyoyin Nijeriya za su iya cim ma ta hanyar hadin gwiwa.

Ribadu ya kuma gargadi masu sayar da haramtattun kayayyaki da cewa ba za su ci gaba da kasuwanci kamar yadda aka saba ba.

Ya kuma ba da tabbacin gwamnati za ta ci gaba da mara baya ga yaƙi da miyagun ƙwayoyi har sai an samu ci gaba mai ma’ana.

"Akwai 'yan Nijeriya nagari da ke aiki don inganta al'umma," in ji shi. "Abin da kwamitin ya samu shaida ne a kan hakan."

Ya kuma bukaci ma’aikatan hukumar da su ci gaba da gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Daga ɓangaren hukumomin

A nata ɓangaren, Darakta Janar ta Hukumar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ta bayyana cewa an kama kwantena 207 ta haramtattun magunguna da na jabu ta hanyar wannan hadin gwiwa.

Ta yaba da shigar da ofishin NSA ya yi cikin lamarin da kuma ɗaukar mataki nan take.

"Idan ba don gaggawar sa hannun NSA ba," in ji ta, "da waɗannan magungunan sun ƙare a kasuwanni kuma sun kai ga mutuwar mata da matasa da yawa."

Shugaban hukumar kwastam, Bashir Adewale Adeniyi, ya bayyana girman aikin a matsayin wanda ba a taba ganin irinsa ba. Ya ce yana nuna tasirin ayyukan cibiyoyi da aka daidaita.

Shi ma sugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa, ya kuma yaba da yadda ofishin NSA ke bayar da tallafin kasafin kudi, wanda ya ce hakan ya taimaka wajen kama mutane da kuma daƙile hanyoyin sadarwa da sufurin miyagun ƙwayoyi.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us