WASANNI
2 minti karatu
Barcelona ta tabbatar da daukar aron Marcus Rashford daga Man United bayan koci ya masa kashedi
Barcelona ta tabbatar da daukar aron Marcus Rashford daga Manchester United, bayan kocin Barca Hansi Flick ya masa kashedi.
Barcelona ta tabbatar da daukar aron Marcus Rashford daga Man United bayan koci ya masa kashedi
/ Reuters
23 Yuli 2025

A yau Barcelona ta tabbatar da ɗaukar Marcus Rashford a matsayin aro daga Manchester United, bayan kammala yarjejeniya tsakanin ɓangarorin biyu.

Barca ta fitar da bidiyon sanarwar da ke nuna ɗan wasan ɗan asalin ingila a cikin wani ɗakin buga waya irin wanda aka saba gani a birnin London.

Rashford ya zama ɗan wasan Ingila na farko da zai buga wa Barcelona wasa tun zamanin Gary Lineker, wanda ya baro can a 1989, shekaru 36 da suka gabata.

Kashedin Flick

Tun da fari, rahotanni daga Sifaniya sun ce kocin Barcelona, Hansi Flick ya gindaya wa Marcus Rashford tsattsauran sharaɗi kafin ya amince da ɗauko ɗan wasan mai shekaru 27.

Flick ya gargaɗi Rashford yayin wata zantawa kai-tsaye da shi, inda ya ce masa dole ya zage damtse ya nemi gurbi a tawagar da za a ringa zaɓa don fara wasa, ta hanyar nuna hazaƙa da juriya.

Kocin ya ce aikin Rashford ba zai tsaya wajen jiran a ba shi ƙwallo ya zura a raga ba, a’a sai ya ringa dawowa baya yana taimakawa wajen tare harin abokan gaba.

Rashford ne da kansa ya nuna kwaɗayin tafiya Barcelona wanda shi ne daililin da ya sa ya ƙi karɓar tayi daga wasu manyan ƙungiyoyi a Turai da Saudiyya.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us