Fiye da Musulmai miliyan daya sun fara Aikin Hajji ta hanyar taruwa a birnin Makka na ƙasar Saudiyya, inda aka saukar da Ƙur'ani ga Annabi Muhammad a shekara ta 610 Miladiyya.
Za a kammala Aikin Hajji a ranar 9 ga watan Yuni tare da Idin Layya, wata ibada ta Musulunci wadda ta samo asali daga lokacin da Allah ya umarci Annabi Ibrahim (AS) ya yi hadaya da ɗansa Isma'il.
Musulmai sun yi imani cewa Annabi Isma'il kakan Annabi Muhammad ne na can nesa.
A cikin addinin Yahudawa da Kiristoci, ɗan Ibrahim da suka yi imanin an yi niyyar yin hadaya da shi shi ne Ishaq, mahaifin Yaqub wanda ya zama kakan ƙabilun Yahudawa goma sha biyu.
Yawancin ibadun Aikin Hajji suna da ma'anar alama ɗaya, suna nufin girmama yadda Ibrahim da ɗansa, da matarsa ta biyu Hajar, mahaifiyar Isma'il ‘yar Afirka, suka sadaukar da kansu ga umarnin Allah.
Amma Hajji kuma wani babban taron shekara-shekara ne na al'ummomin Musulmai daga kowane matsayi na zamantakewa da jinsi, da kuma kasashe daban-daban.
Kalmar Hajji tana nufin “zuwa bauta wa Allah a wata tafiya ta musamman” don yin ibadu, ciki har da ɗawafi, ma’ana zagaye Ka’aba, wuri mafi tsarki a Musulunci, in ji Dr. Ekrem Keles, tsohon shugaban Hukumar Addini ta Turkiyya.
Hajji yana girmama silsilar annabawa daga Annabi Adam da Ibrahim zuwa Annabi Muhammad, in ji shi.
Bayan gwagwamayar da Annabi Ibrahim, mai kare tauhidi ya yi da Namrud mai goyon bayan bautar gumaka, sai Annabin Allah ya yanke shawarar barin arewacin Mesopotamiya, wanda yanzu yake a kudu maso gabashin Turkiyya, zuwa wani wuri mai nisa wanda aka sani da Makka, in ji Keles a hirarsa da TRT World.
Annabi Ibrahim ya mayar da Hajar da jaririnta Isma'il zuwa Makka, wuri mai hamada a lokacin.
Bisa ga al'ada, Annabi Ibrahim ya bar Hajar da ɗansu a Makka su kaɗai. Amma kafin ya tafi, ya yi addu’a ya roƙi Allah:
“Ya Ubangijinmu! Na zaunar da wasu daga cikin zuriyata a kwarin da ba shi da shuka, kusa da GidanKa Mai Tsarki, ya Ubangijinmu, domin su tsayar da salla. Don haka Ka sanya zuƙatan mutane masu imani su karkata zuwa gare su. Ka kuma azurta su da 'ya'yan itatuwa, don su kasance masu godiya.” (Al-Qur'ani, Suratul Ibrahim: 37)
Wannan Gidan Mai Tsarki shi ne Ka'aba, wanda aka fara ginawa da Annabi Adam, kuma daga baya Annabi Ibrahim tare da taimakon ɗansa Isma'il suka sake ginawa, bisa ga al'adar Musulunci.
“Al'adun Hajji suna nuna cewa addu'ar Ibrahim ta samu karɓuwa daga Allah saboda Musulmai suna son ganin Ka'aba [inda Hajar da Isma'il suka zauna], da sauran wurare masu muhimmanci na addini da ke da alaƙa da Ibrahim a kusa da Makka, kuma suna kewarsu sosai bayan sun bar waɗannan wuraren,” in ji Keles.
A lokacin Hajji, Musulmai kuma suna tafiya tsakanin Safa da Marwah, duwatsu biyu waɗanda Hajar ta yi gudu cikin fargaba a tsakaninsu don neman ruwa ga Isma'il.
“Kamar yadda Hajar ta yi, yanzu dukkan Musulmai suna tafiya a cikin fata don tuna ƙoƙarinta mai ban tausayi na neman ruwa a wannan wuri tsakanin Safa da Marwah, wanda ake kira sa’ayi a cikin ibdaun Hajji, wani muhimmin bangare na ibadar Hajji,” in ji Keles.
A ƙarshe, godiya ga rahamar Allah, Hajar, wata mace baƙar fata wadda ta taɓa zama baiwa, ta gano wani tushen ruwa, wanda ake kira Ruwan Zamzam. Tun daga lokacin, Zamzam ya kasance yana shayar da miliyoyin Musulmai.
Hajji ba kawai wata ƙwarewa ce ta mutum don zurfafa imani ba, amma kuma wani nau'in ibada ce ta haɗin-kai, in ji Faruk Gorgulu, mataimakin farfesa na Tafsiri a Jami’ar Duzce.
Ƙur'ani ya sanya Hajji wajibi ga dukkan Musulmin da Allah Ya ba wa iko. Yana daya daga cikin ginshikan addinin Musulunci, kamar salla da azumi.
Wannan labarin an fara wallafa shi a watan Yunin 2024 kuma an sabunta shi don nuna sabbin bayanai na Hajjin 2025.