NIJERIYA
5 minti karatu
Muhimman abubuwa 5 da Shugaba Tinubu ya yi magana a kai bayan ya cika shekara 2 a mulkin Nijeriya
Daga cikin abubuwan da Shugaba Tinubu na Nijeriya ya yi magana a kai har da batun irin wahalhalu da matsalolin tattalin arziƙi da ya gada daga gwamnatin baya da kuma yadda ya shawo kansu.
Muhimman abubuwa 5 da Shugaba Tinubu ya yi magana a kai bayan ya cika shekara 2 a mulkin Nijeriya
Shugaba Tinubu na Nijeriya / Nigeria Presidency
29 Mayu 2025

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa irin jerin garambawul ɗin da gwamnatinsa ta yi a shekaru biyu da suka gabata ta fannoni daban-daban, a halin yanzu sun kasance wani tubali na kawo ci gaba ga makomar ‘yan Nijeriya.

Shugaban ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, bayan cika shekara biyu a kan karagar mulki.

Shugaba Tinubu, wanda aka rantsar a matsayin shugaban ƙasa a ranar 28 ga Mayun 2023, ya bayyana cewa tsare-tsarensa na Renewed Hope Agenda na aiki tuƙuru domin rage tsadar rayuwa da ƙara haɓaka tattalin arziƙi da samar da tattalin arziƙi mai inganci wanda zai taimaki kowane ɗan Nijeriya da kuma jawo zuba jari.

Ga wasu daga cikin abubuwan da Shugaba Tinubu ya yi magana a kansu a sanarwar da ya fitar sun haɗa da:

Garambawul kan tattalin arziƙi

A jawabin nasa na buɗewa, Shugaban Ƙasar ya yi bayani kan irin wahalhalu da matsalolin tattalin arziƙi da ya gada daga gwamnatin baya inda ya ce hakan ne ya sa dole ya yi garambawul.

“Mun ɗauki matakai biyu waɗanda suka kasance tilas mu ɗauke su domin dakatar da ƙasarmu daga ci gaba da faɗawa cikin bala’i — kawo ƙarshen tallafin man fetur da kuma samar da tsarin canjin kuɗaɗen waje na bai-ɗaya,” kamar yadda ya bayyana.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa waɗannan matakan duk da cewa da farko sun zo da ƙalubale ga ‘yan Nijeriya da dama, amma a halin yanzu sun kawo daidaito a fannin tattalin arziƙi da rage hauhawar farashi da kuma jawo zuba jari da ya kai fiye da dala biliyan takwas.

A cewar Shugaban, ɓangaren mai da iskar gas ya samu farfaɗowa sosai, inda yadda ake haƙo mai ya ƙaru da kaso 400 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar 2021.

Gwamnatin ta kuma bayar da rahoton jimillar kuɗaɗen da aka samu na ɗanyen mai daidai da hasashen kasafin kuɗi da kuma rage giɓin kasafin kuɗi daga kashi 5.4% na GDP a shekarar 2023 zuwa kashi 3.0% a shekarar 2024.

Sauya tsarin haraji da sauyi kan yadda ake kashe kuɗin gwamnati

Wani babban jigo a wannan jawabin na Shugaban Ƙasa shi ne batun sauya fasalin karɓar haraji da kuma yadda ake kashe kuɗin a ƙasar.

Shugaban ya bayyana cewa an samu ƙaruwa a adadin haraji zuwa ma’aunin tattalin arziƙin ƙasa daga kaso 10 cikin 100 zuwa 13.5 a ƙarshen 2024, inda ya ce an samu hakan ne sakamakon yadda aka ƙara inganta tsarin karɓar haraji.

Ya bayyana cewa an kawar da tsarin da ake da shi a baya na saka haraji daban-daban sannan kuma ya ce an cire haraji kan muhimman kayayyaki waɗanda suka haɗa da abinci da ilimi da kiwon lafiya da kuɗin haya da sufuri .

Samar da ingantaccen tsaro

Shugaba Tinubu ya ƙara jaddada wa ‘yan Nijeriya kudurinsa na ci gaba da samar da tsaro a ƙasar.

Ya jinjina wa jami’an tsaron ƙasar dangane da irin gudunmawar da suke bayarwa inda ya ƙara jaddada batun haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro daban-daban da ake da su a ƙasar da kuma ƙara inganta aikin ta hanyar tattara bayanan sirri.

“A wasu sassan arewa maso yamma da a baya ke hannun ‘yan ta’adda, sojojinmu sun dawo da zaman lafiya. Manyan tituna sun ƙara samun tsaro, kuma an kuɓutar da ‘yan kasar da aka sace,” kamar yadda ya ƙara da cewa.

Shugaban Ƙasar ya kuma lashi takobin ci gaba da kawar da barazanar ta’addanci a ƙasar.

Ayyukan ci gaban al’umma da bayar da tallafi

A jawabin na Shugaban Ƙasar, ya lissafo irin ayyukan da gwamnatinsa ta yi na ci gaban al’umma da tallafi tun daga ɓangaren kiwon lafiya da ilimi da tallafa wa matasa.

Shugaban ya bayyana cewa ana aikin farfaɗo da asibitocin kiwon lafiya a matakin farko fiye da 1,000 a faɗin ƙasar da kuma ƙirƙiro da sabbin cibiyoyin magance cutar kansa.

Haka kuma shugaban ya bayyana cewa an faɗaɗa tsarin inshorar lafiya daga mutum miliyan 16 zuwa miliyan 20.

Sannan kuma ya ce an yi wa mata fiye da 4,000 tiyatar haihuwa kyauta da kuma yin rangwamen kuɗi ga masu zuwa wankin ƙoda.

Ta ɓangaren ilimi kuwa, shugaban ya bayyana cewa an faɗaɗa tsarin bayar da bashin karatu ga ɗalibai marasa galihu, yayin da shirye-shiryen da suka shafi matasa kamar Innovate Naija da NASENI suke tallafa wa ƙanana da matsaƙaitan masana’antu.

Samar da ababen more rayuwa, inganta noma da makamashi

Shugaban ƙasar ya zayyano irin ɗumbin ci gaban da aka samu ta ɓangarem ababen more rayuwa, daga ciki har da gina manyan hanyoyi a faɗin yankunan ƙasar shida.

A ɓangaren noma, shugaban ya jaddada aniyarsa ta ci gaba da samar da isashen abinci ta hanyar bayar da tallafi ta ɓangaren zamanantar da harkar noma,

Haka kuma ya bayyana cewa gwamnatinsa na ci gaba da aiki domin samar da isashiyar wutar latarki da kuma zuba jari ta ɓangaren samar da wuta ta hanyar hasken rana.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us