Yara 'yan tara na farko a duniya sun shekara hudu
Yara 'yan tara na farko a duniya sun shekara hudu
Yara 'yan tara 'yan ƙasar Mali da su kaɗai suka taɓa rayuwa a duniya sun cika shekara huɗu, inda suka dinga samun saƙonnin taya murna daga ƙasarsu da ma sauran ƙasashen duniya.
6 Mayu 2025

Yaran ‘yan tara ‘yan iyalan Cissé da suka hada da 'yan mata biyar da maza hudu, an haife su ne a matsayin bakwaini ta hanyar tiyata a birnin Casablanca na Moroko a ranar 4 ga Mayun 2021, lamarin da ya jawo hankalin duniya baki daya.

Haihuwarsu wata mu'ujiza ce ta likitanci, inda kowanne jariri daga cikinsu ya kasance yana da nauyin tsakanin kilo 0.5 zuwa 1.

Da farko an yi tunanin za a haifi jarirai bakwai ne, amma iyayensu sun yi mamakin samun jarirai tara.

Iyayen jariran, Halima Cissé da Abdelkader Arby, sun shirya bikin cikar jariran shekaru hudu a ranar Lahadi, 4 ga watan Mayu.

"Kowa yana tambayata sirrina; ba ni da wani sirri. E, gaskiya, ba ni da wani sirri," in ji mahaifiyarsu Halima Cissé ga TRT Afrika a ranar bikin cika shekararsu huɗu da haihuwa.

An sanya wa 'yan matan suna Kadidia da Fatouma da Hawa, Adama, da Oumou, yayin da aka sanya wa mazan suna Mohammed da Oumar, Elhadji, da Bah. Sun kwashe watanni tara a Moroko, inda aka haife su, kafin a kai su Mali.

Albarka daga Allah

Rayuwarsu ta samu nasara ne saboda kulawar ƙwararrun likitoci daga wata tawaga ta musamman. Rainon yaran ya kasance cike da kalubale, amma iyayen sun samu goyon baya da yabo daga mutane da dama.

Yayin da suke bikin cikar shekaru hudu, yaran suna ci gaba da jan hankalin mutane a duniya baki daya. Labarinsu yana nuna ci gaban kimiyyar likitanci da kuma juriya ta ruhin dan’adam.

Kwarewar iyalin ta kuma kara wayar da kan mutane game da haihuwar jarirai masu yawa da kuma muhimmancin samun ingantacciyar kulawar lafiya.

Labarin Halima Cissé da Abdelkader Arby yana zama shaida ga karfin fata da jajircewa.

"Wannan shi ne nufin Allah. Mu masu imani ne a wannan fannin. Albarka ce daga Allah Madaukaki, wanda ya yanke wannan hukunci. Kuma wannan abu ne na musamman a gare mu.

“Dole ne mu ba juna kulawa mafi kyau da za mu iya da kuma nuna soyayya. Kuma kowanne yana da wani abu na musamman," in ji mahaifinsu Abdelkader Arby ga TRT Afrika.

Hakkin kowa

Yayin da yaran ke girma, labarinsu zai ci gaba da zama abin koyi da jan hankali ga mutane a duniya baki daya.

"A al'adance, haihuwar tagwaye a cikin al'ummominmu tana zama abin da dukkan al'umma ke kula da shi. Yanzu, muna magana ne a kan yara tara," in ji Baba Seydou Bally, shugaban Gidauniyar Bally, wanda ke tallafa wa iyalin.

"Za mu yi iya kokarinmu don tabbatar da cewa yaran za su samu kyakkyawar tarbiyya ta zamantakewa," in ji Bally.

"Ku yi la’akari da nauyin da haihuwar yaran nan da rainonsu ya ɗora a kan iyayen. Don haka, ya zama wajibi a gare mu a matsayin 'yan’uwan wannan iyali, ya zama wajibi a gare mu a matsayin 'yan Afrika, mu taimaka don yaran su girma cikin kwanciyar hankali," ya faɗa.

Haihuwar waɗannan yara tara ba iyalan Cissé wata tunatarwa ce game da kyawun rayuwa da kuma rikitarwarta. Tare da soyayya da kulawar iyayensu, yaran suna ci gaba da yin tasiri a duniya.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us