NIJERIYA
3 minti karatu
Hukumomin tsaro sun hana bukukuwan Babbar Sallah a Kano
A lokacin bukukuwan ƙaramar sallah da ta gabata ma, rundunar ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro a jihar Kano sun haramta hawan dawaki, saboda dalilai na tsaro kamar yadda suka bayyana.
Hukumomin tsaro sun hana bukukuwan Babbar Sallah a Kano
Shugabannin hukumomin tsaron Kano bayan wani taro da suka gudanar
4 Yuni 2025

Hukumomin tsaro a jihar Kano da ke arewacin Nijeriya sun sanar da hana duk wani na’ui na bukukuwan sallah da suka haɗa da hawan dawaki da sarki yake yi.

Wata sanarwa da kakain rundunar ‘yan sandan jihar Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a ranar Talata a madadin sauran hukumomin tsaro a jihar, ta ce haramcin da aka yi na hawan ƙaramar sallah har yanzu yana aiki, saboda har yanzu akwai barazanar tsaron da ta sa aka ɗauki matakin.

“Don haka rudunar tana jaddada cewa hana duk wani nau’i na hawan daba da aka yi a jihar har yanzu yana aiki, kuma za a tabbatar da aiki da shi yayin bukukuwan Babbar Sallah, saboda barazanar da ta sa aka ɗauki matakin har yanzu tana nan,” a cewar sanarwar ta Kiyawa

Sanarwar ‘yan sanda kusan ta zo ne ‘yan sa’o’i bayan da Masarautar Kano ta umarci duka masu riƙe da sarauta da hakiman Sarki Muhammadu Sanusi su shiga birnin da dawakansu don shirin gudanar da hawan sallah.

‘Barazanar tsaro’

A cewar sanawar ta ‘yan sanda dai an ɗauki matakin ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa “wasu ɓata gari da masu ɗaukar nauyinsu na shirin yin amfani da hawan sallar don kawo matsala ga zaman lafiya da harkokin tsaro, irin wanda aka fuskanta da Ƙaramar Sallah.

Bisa haka ne sanarwar ta zayyana jerin abubuwan da aka hana

  • Babu kowane irin hawan dawaki (Kilisa)

  • Babu tseren motoci ko tuƙin ganganci

  • Babu ɗaukan makami ba bisa ƙa’ida ba ko kuma wasa da makaman

  • Babu ɗaukan makamai ko wasu abubuwa masu haɗari

A lokacin bukukuwan karamar sallah da ta gabata ma, rundunar ‘yan sandan da sauran hukumomin tsaro a jihar Kano sun haramta hawan dawaki, saboda dalilai na tsaro kamar yadda suka bayyana.

Sai dai an samu hatsaniya har aka kashe mutum ɗaya aka kuma jikkata wani yayin da Sarki Muhammdu Sanusi II yake komawa fada, bayan halartar sallar idi.

Rundunar ‘yan sandan ta ce ta kama wasu da ake zargi da aikata laifin.

Lamarin ya sa rundunar ‘yan sanda ta ƙasa gayyaci Sarki Sanusi Abuja kan dalilan da suka sa ya yi ‘hawa’ duk da umarnin da jami’an tsaro suka bayar.

Sai dai fadarsa ta musanta cewa ya yi hawa, ya dai fita idi ne ya koma fada kamar yadda aka saba.

Tun bayan matakin da gwamnatin kano ta ɗauka a watan Mayun 2024 na mayar da Sarki Sanusi Sarautar Kano da sauke Sarki Aminu Ado Bayero wanda gwamnatin Ganduje ta naɗa, ake samun taƙaddama kan halastaccen sarkin na Kano, har ma a yanzu ake ganin akwai sarakai biyu a Kano.

Wasu dai na zargin gwamnatin tarayyar ƙasar da jami’an tsaro da mara wa Sarki Aminu baya a taƙaddamar da ake yi kan sarautar, sai dai gwamnatin ta musanta wannan zargin, yayin da jami’an tsaro ke cewa suna ƙoƙarin tattabar da doka da oda ne da mutunta umarnin kotu da ya ce ‘kowa ya tsaya a inda ake’ har sai an yanke hukunci.

A yanzu haka akwai shari’u daban-daban a gaban kotuna ciki har da Kotun Ƙoli don neman warware takaddamar wane ne halastaccen sarkin Kano. Kuma a yanzu hankula sun karkata kan Kotun ta Ƙoli ne wacce za ta raba gardama.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us