Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Haka Fidan ya soki kisan kiyashin da Isra’ila ke aikatawa a Gaza a lokacin da yake jawabi a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, inda ya ce rikicin ya mayar da yankin zuwa ‘sansanin musgunawa jama’a’ inda ya zargi Isra’ila da tsara kai wa fararen-hula hare-hare.
“A yayin da muka taru a wannan zauren, kisan kiyashin da Isra’ila ke aikatawa kan Falasɗinawa na ci gaba babu ƙaƙƙautawa,” in ji Fidan a ranar Laraba.
“Fiye da mutane miliyan biyu na shan matsananciyar wahala a Gaza wadda ba a bayyana wa duniya.”
Ya ambato raba jama’a da dama da matsugunansu, rusau a wurare da yawa, da kuma toshe hanyoyin kai kayan agaji da gangan.
“Ana karkashe fararen-hula a tare da bambance wa ba a wuraren bayar da kayan agaji a yayin da suke ƙoƙarin karɓar abinci da ruwa. Ana amfani da yunwa a matsayin makami a yaƙin,” in ji shi.
‘Makamai da aka gina da nuna tsana’
Fidan ya zargi isra’ila da karya duk wasu manyan dokokin ƙasa da ƙasa.
“Babu bambanci ko yaro ne ƙarami kai da ke ɗauko ruwa ko uwa da ke neman abinci - kawai Isra’ila za ta kashe ka,” in ji shi.
“Wannan makami ne da aka gina da tsana.”
Ya yi gargaɗin cewa rikicin jinƙai a Gaza ya ta’azzara tare da zama wata jarrabawar halayyar ta duniya.
“Wasu sun zaɓi kawar da kawunansu. Ba za a ci gaba da aikata hakan ba.”
Ministan ya jaddada cewa Majalisar Ɗinkin Duniya ce kaɗai za ta iya tabbatar da an kai kayan agaji lami lafiya.
“Manyan ginshiƙan jinƙan ɗan’adam su ne, rungumar kowa, rashin ɗaukar ɓangaranci da kuma ‘yanci, waɗanda dole ne a kiyaye su.”
Hatsarin faɗaɗar rikicin
Fidan ya kuma yi gargaɗin cewa yaƙin da sojojin Isra'ila ke yi na kawo hatsarin faɗaɗar rikici a yankin.
“Wannan dabarar ta wuce-gona-da-iri ta shafi Falasdinu kadai ba ne, har ma da Lebanon, da Syria da kuma Iran,” in ji shi.
"A Siriya, hare-haren Isra'ila na barazana ga kwarya-kwaryar zaman lafiya mai wahala."
Ya kuma buƙaci ƙasashen duniya da su hana ruruwar wutar rikicin tare da tabbatar da cewa Syria ba za ta koma cikin ruɗani ba.
Fidan ta nanata goyon bayan Turkiyya don kafa cikakkiyar ƙasar Falasɗinu mai ‘yanci kuma mamba a Majalisar Ɗinkin Duniya.
"Wannan yana da mahimmanci don samun dauwamammen zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya," in ji shi.
A ƙarshe ya yi kakkausar suka ga Kwamitin Tsaro na MDD.
"Ya gaza yi wa al'ummar Gaza komai. Ya kasa kare mutuncin bil'adama. Wannan ba kawai gaggawar ayyukan jinƙai ba ce - gwaji ne na bil'adama baki ɗaya."
"Abin da ya kamata a yi a bayyane yake ƙarara: dakatar da injin yaƙin Isra'ila, dakatar da fin ƙarfin fuskantar hukunci, tabbatar da tsagaita wuta nan-take, da isar da kayan agajin jinƙai ba tare da wata tangarda ba, da kuma sabunta alkawari kan samar da kasashe biyu-yanzu."