TURKIYYA
1 minti karatu
Erdogan ga Stocker: Bai kamata a yi watsi da damar kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine ba
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi magana game da dangantakar ƙasashen biyu da kuma batutuwan yankin da na duniya a tattaunawarsa da Shugaban Austria Christian Stocker.
Erdogan ga Stocker: Bai kamata a yi watsi da damar kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine ba
Erdogan emphasised that delivering urgent humanitarian aid to Gaza as soon as possible was of the utmost importance. / AA
10 Yuli 2025

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya bayyana cewa bai kamata a yi watsi da damar kawo ƙarshen yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine ba.

A wata tattaunawa ta wayar tarho da Shugaban Austria, Christian Stocker, Erdogan ya magana kan dangantakar ƙasashen biyu, tare da batutuwan yankin da na duniya baki ɗaya, in ji Hukumar Sadarwa ta Turkiyya a ranar Alhamis.

A yayin tattaunawar, Erdogan ya jaddada muhimmancin isar da agajin jin ƙai cikin gaggawa zuwa Gaza a matsayin abin da ya fi muhimmanci a halin yanzu.

Dangane da Siriya, ya bayyana cewa Turkiyya na ci gaba da ƙoƙarinta na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar, tare da ƙara inganta walwala ta zamantakewa da tattalin arziki domin sauƙaƙa komawar 'yan gudun hijirar Siriya zuwa gidajensu.

Shugaban ya kuma ce ya kamata Turkiyya da Austria su yi amfani da damar da ke akwai wajen kasuwanci da zuba jari yadda ya kamata, kuma za su ci gaba da ɗaukar matakai don ƙarfafa haɗin kai.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us