Ma’aikatar Harkokin Mata ta Jihar Katsina da ke Nijeriya ta sanar da ƙaddamar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa jami’an hukumar Hisbah a jihar na cin zarafin wata mata.
A makon jiya ne aka riƙa yaɗa hirar da aka yi da wata mata inda ta zargi jami’an na Hisbah da lakaɗa mata duka, lamarin da ya kai ga karya mata ƙafa da lahanta mata kunne.
Sai dai a sanarwar da ma’aikatar harkokin matan ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa ta fara gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa jami’an na Hisbah, tana mai ƙara wa da cewa za ta yi binciken bisa gaskiya kuma za a yi shi a bayyane.
“Ma’aikatar Harkokin Mata ta Jihar Katsina ta samu wani rahoto mai tayar da hankali da ke yawo a shafukan sada zumunta, wanda ya ƙunshi shaidar da wata mata ta bayar a wani bidiyo inda ta zargi wasu mutane da ke da alaƙa da Hukumar Hisbah da nuna mata rashin imani.
“A matsayinmu na ma’aikatar da ke da alhakin kare haƙƙi da martabar mata da ‘yan mata a Jihar Katsina, muna Allah wadai da babbar murya ga duk wani nau’in cin zarafi da ake yi wa mata, musamman waɗanda ake yi da sunan koyar da tarbiyya. Babu wata mace, ko kuma wani mutum, da ya kamata a yi wa irin wannan cin mutuncin. Wannan lamarin, kamar yadda ake zargi, a bayyane ya zama batu na cin zarafi kan mata kuma dole a magance shi cikin gaggawa,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
“Ma’aikatar tana ci gaba da bincike sosai kan lamarin tare da haɗin gwiwar kwamandan hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, Dakta Aminu Usman, wanda ya bayyana kudurinsa na tabbatar da yin komai a bayyane kuma bisa gaskiya.
“A halin yanzu muna tattara cikakkun bayanai kuma za mu miƙa sakamakon bincikenmu ga hukumomin da suka dace don ɗaukar mataki. Har ila yau, ma'aikatar za ta bayar da taimako ta fannin shari’a da na lafiya kan wadda ake zargi an ci zarafinta da wasu da abin ya shafe su,” kamar yadda ta ƙara da cewa.