Mambobin ƙungiyar ta'addanci ta PKK sun fara ajiye makamai a lardin Suleymaniye na ƙasar Iraki a ranar Juma’a, wani muhimmin ci gaba da ya yi daidai da ƙoƙarin Ankara na cim ma burin kawar da ta'addanci.
Bayan ayyukan yaƙi da ta'addanci masu ƙarfi da jami'an tsaron Turkiyya suka gudanar, PKK ta sanar a watan Mayu cewa za ta rushe kanta tare da ajiye makamai, wanda ya zama babban ci gaba a cikin gwagwarmayar da ƙasar ta shafe shekaru da dama tana yi da ta'addanci.
A lokaci guda, gwamnatin Turkiyya ta faɗaɗa yaƙin ta'addanci zuwa fagen diflomasiyya.
Shekarun da aka shafe ana matsa lamba mai ɗorewa kan abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa — musamman a Turai da Gabas ta Tsakiya — sun haifar da kyakkyawan sakamako.
Ikon PKK na gudanar da ayyuka cikin sauƙi a manyan biranen ƙasashen waje, da samar da kuɗaɗe ta hanyar muna-munar siyasa ya ragu sosai.
Tasirin siyasar ƙasa da ƙasa na Turkiyya da ke ƙaruwa ya sa ƙasashen duniya suna ɗaukar damuwarta da muhimmanci.
Ta hanyar haɗin gwiwar tattalin arziki, diflomasiyyar makamashi, da haɗin kai na yankuna, Ankara ta yi nasarar rage hanyoyin tallafin PKK a ƙasashen waje.
Mai magana da yawun jam’iyyar Adalci da Ci Gaba (AK Party) ta Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bayyana a ranar Laraba cewa za a kammala ajiye makaman a cikin ‘yan watanni.
A wata hira da gidan talabijin na NTV, Omer Celik ya bayyana cewa wata tawagar tabbatarwa — da jami’an leƙen asiri na Turkiyya da sojoji suka haɗa — za su sa ido kan tsarin ajiye makaman.
“Ya kamata a kammala a tsarin ajiye makamai (a Iraki) a cikin watanni uku zuwa biyar ... Idan ya zarce wannan lokaci, zai iya zama mai rauni da jawo cikas ga zaman lafiya,” in ji Celik.
Fiye da shekaru 40, Turkiyya tana yaƙi da PKK, wadda ta kashe fiye da mutum 40,000 ta hanyar hare-hare kan fararen hula da jami’an tsaron Turkiyya.