NIJERIYA
2 minti karatu
Nijeriya za ta karɓi magungunan cutar kuturta daga WHO bayan jinkiri na tsawon lokaci
Kididdigar WHO ta nuna cewa Nijeriya na ɗaya daga cikin ƙasashe 12 da ke bayar da rahoton kamuwa da cutar inda ake samun tsakanin mutum 1,000 zuwa 10,000 a duk shekara masu kamuwa cutar.
Nijeriya za ta karɓi magungunan cutar kuturta daga WHO bayan jinkiri na tsawon lokaci
Ana iya magance cutar bayan shan magani na wani lokaci, amma idan ba a shan magani, cutar na ƙaruwa / Reuters
8 Maris 2025

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce za ta aika da magungunan cutar kurtta zuwa Nijeriya a ƙarshen makon nan bayan jinkirin da aka samu na gwaje-gwaje, lamarin da ya jawo dubban masu fama da cutar daga ciki har da yara ba su samu magungunan da suka kamata na kare cutar ba.

Nijeriya wadda ita ce ƙasar Afirka da ta fi yawan jama’a na bayar da rahoton samun aƙalla mutum 1,000 da cutar kuturta a duk shekara, wadda cuta ce da ke kama fatar jiki da jijiyoyi da idanu.

Ana iya magance cutar bayan shan magani na wani lokaci, amma idan ba a shan magani, cutar na ƙaruwa, idan take jawo gyambo da kuma nakasa kamar makanta da shanyewar rabin jiki. Haka kuma masu fama da cutar na fuskantar hantara.

Sai dai magungunan da Nijeriya take da su na cutar sun ƙare a farkon shekarar 2024 sakamakon jinkirin da aka samu na sabbin dokokin cikin gida da aka samar na gwaje-gwaje kan magungunan da ake shigar da su cikin ƙasar.

Jinkirin jigila

 Jinkirin wanda ya jawo wahalhalu a Nijeriya, misali ɗaya ne daga ake samu a tsarin duniya wanda ke faruwa a ƙasashe da dama waɗanda suka haɗa da Indiya da Brazil da Indonesia a ‘yan shekarun nan, kamar yadda wakili na musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya kan cutar kuturta ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Wani mai magana da yawun hukumar ta WHO ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa Nijeriya ta daina samun magungunan cutar kuturta, kuma hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya da ke shirya jigilar magunguna ta bukaci a yi watsi da sabuwar manufar gwajin. A watan Janairu an ba da izinin.

 “An tabbatar da jigilar magungunan kuturta daga Indiya a ranar 8 ga Maris, tare da isowa Nijeriya ranar 9 ga Maris,” in ji kakakin a saƙon da ya aiko ta adireshin email.

Kididdigar WHO ta nuna cewa Nijeriya na ɗaya daga cikin ƙasashe 12 da ke bayar da rahoton kamuwa da cutar inda ake samun tsakanin mutum 1,000 zuwa 10,000 a duk shekara masu kamuwa cutar, bayan Brazil, Indiya da Indonesia. Kowace ƙasa tana buƙatar allurai na kuturta, wanda magani ne na kafso da ake amfani da shi na tsawon watanni 12, daga WHO kowace shekara.

 

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us