WASANNI
1 minti karatu
Ko za a samu mai sayen Andre Onana kan dala miliyan 41 daga wajen Manchester United?
Manchester United ta saka wa golanta, Andre Onana farashin tayi na dala miliyan 41, bayan da Monaco ta Faransa ta nuna sha’awar ɗaukar sa.
Ko za a samu mai sayen Andre Onana kan dala miliyan 41 daga wajen Manchester United?
/ AP
8 Yuli 2025

Manchester United ta saka wa golanta, Andre Onana farashin tayi na dala miliyan 41, bayan da Monaco ta Faransa ta nuna sha’awar ɗaukar mai tsaron gidan.

Farashin da aka sa wa Onana wanda ɗan asalin Kamaru ne, ya yi tsada ga Monaco duk da ƙungiyar ta ce za ta ci gaba da saka idon don ganin abin da hali zai yi.

Sai dai da wuya ta iya miƙa sabon tayi matuƙar farashin bai sauko ba.

Duk da cewa Koci Ruben Amorim zai so ya sayar da golan mara tagomashi, alamu na nuna Onana zai ci gaba da zama a Man United.

A yanzu United na da burin ɗauko golan Aston Villa, Emiliano Martinez, duk da Andre Onana yana da kwantiragi da Manchester United har zuwa 2028.

A bara Onana ya buga wasanni 50 a duka gasanni, inda a wasa tara kacal ne ba a sha shi ƙwallo ba.

Hakan na daga cikin dalilan da United ta ƙare kakar bara a mataki na 15 a teburin Gasar Firimiya.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us