TURKIYYA
4 minti karatu
Emine Erdogan ta samu lambar yabon ‘Mace Shugaba da ta fi zarra a duniya'
An karrama uwar gidan Shugaban Ƙasar Turkiyya Emine Erdogan ne a birnin Istanbul saboda manufarta ta taimakon jinƙai da gwagwarmaya a duniya
Emine Erdogan ta samu lambar yabon ‘Mace Shugaba da ta fi zarra a duniya'
Maiɗakin shugabna ƙasar Turkiyya Emine Erdogan ta samu lambar yabon na duniya ne a birnin Istanbul saboda yadda take gwagwarmaya kan tausayi da haɗin kai da kuma tallafin jinƙai a duniya gabaɗaya / AA
15 Afrilu 2025

Mai ɗakin shugaban ƙasar Turkiyya Emine Erdogan ta samu lambar yabon ‘Mace Jagora Da Ta Yi Zarra a Duniya ‘ daga taron masu ba da tallafin jinƙai na duniya, da aka yi a birnin Istanbul wanda Ƙungiyar Musulmai masu ba da tallafi ta duniya suka shirya.

A jawabinta na ranar Litinin, Erdogan ta bayyana farin cikinta cewa birnin Istanbul ne ya sake karɓar baƙuncin taron— birnin da ta bayyana a matsayin wata alama ta tausayi inda alheri ke a manne a jikin gine-gine.

Ta yi nazari game da ayyukan ba da kyauta na tarihi da ke da asali a al’adar daular Usmaniyya, daga gidauniya mai taimaka wa sabbin amare har zuwa aikin raba ruwan sanyi a lokacin zafi. "Waɗannan ayyukan sun nuna cewa a lokacin da zuciya take a cike da alheri, duniya za ta zamanto tamkar Aljanna," in ji ta.

Erdogan ta yi gargadin cewa halin kirki na mutane ya raunana, tana mai cewa, "an bar bin gaskiyar zuƙatanmu cikin duhu."

Bala’in jinƙai a Gaza

Erdogan ta lissafa yaƙen-yaƙen da ake yi a duniya yanzu — daga yaƙin Syria da aka shafe shekara 13 ana yi zuwa bala’in jinƙai a Gaza.

A lokacin da take ishara ga wasu alƙalluma da ma’aikatar lafiya ta Gaza ta fitar kwanan nan waɗanda suka tabbatar da shahadar mutum 50,000, Erdogan ta ce alƙalluman abu “kunya ne ga bil’adama.”

Ta ƙara da cewa: “Shafuka 474 na takardar sun ƙunshi sunayen yara 15,613; yayin da shafuka 27 ke cike da jarirai da ba su yi bikin zagoyawar ranar haihuwarsu na farko ba.”

Ta yi kira ga mutane su ci gaba da kasancewa masu fata, inda ta kawo hadisin Manzon Allah (SAW) inda ya ce: “Ko da ƙarshe duniya ya zo, ka dasa bishiya ta ƙarshe da ke hannunka.”

'Kamar bishiyar zaitun, muna faɗaɗa rassanmu ga bil’adama'

Da take bayyana yadda Turkiyya ta dage kan ba da tallafi ga duniya, Erdogan ta ce: “Turkiyya daya ce daga cikin ƙasashen da suka fi ba da tallafin jinƙai a duniya kuma wadda ta fi kyauta idan aka kwatanta da ƙundin shigar ƙasa. Kamar bishiyar zaitun, muna miƙa rassanmu ga bil’adama.”

Ta ƙara da cewa a halin ynazu Turkiyya tana bai wa ‘yan gudun hijira miliyan hudu, yawanci daga Syria,  mafaka kuma tana tura tallafi ga ƙasashe kamar Sfaniya da Cuba da Vietnam da kuma Madagascar.

“Salon ba da tallafinmu ba kyauta bisa nuna fifiko ba, amma bisa ‘yanuwantaka — ba ma lura da launin fata ko addini ko ƙabila,” in ji ta.

Erdogan ta jaddada hanyar ba da tallafi bisa ci-gaba da Turkiyya ke bi, daga ababen samar da kiwon lafiya zuwa koyar da sana’a. Ta jaddada muhimmancin haɗin kai na dabaru tsakanin ƙasashen Musulmai, inda ta kawo wani hadisi mai cewa: “Munimi da wani muni tamkar bulo ɗin gini ne da ɗaya ke ƙarfafa ɗaya.”

Ta goyi bayan mafita mai ɗorewa da ta wuce  ba da tallafi na wucen gadi kuma maimakon haka a mayar da hankali kan sake gini da farfadowa da kuma ƙrfafa al’ummomi.

Bayan shaida matsalolin jinƙai kai tsaye — a Pakistan da Somalia da Arakan — Erdogan ta ce mutanen da suke ba da taimako cikin irin waɗannan rikice-rikicen “sun haskaka da hasken tausayi da babu irinsa.”

“Ba da kyauta ita ce mafaka da ta fi kwantar da hankali a duniya,” in ji ta.

Goyon bayan duniya da rawar da Turkiyya ke takawa

A wani saƙon bidiyo, Shugabar Ƙungiyar Musulmai Masu Ba Da Ta Duniya Sheikha Aisha Bint Faleh Al Thani ta yaba wa ƙoƙarin ba da agaji na Turkiyya a Gaza da kuma jagorancin Erdogan.

Ta ce al’adar Turkiyya ta rungumi bambance-bambance kuma ilimi da ƙirƙira da tausayi ne suka tsara ta — wani gadon da shugaban yanzu ya ci gaba da shi.

Tsohon Firayim Minista na Farko na Scotland Humza Yousaf shi ya yaba wa agajin da Turkiyya ke bayarwa da kuma muryar Emine Erdogan da take ɗagawa a madadin waɗanda ake dannewa.

“Kin yi magana a lokacin da mutane da dama suka zaɓi yin shiru,” kamar yadda ya shaida mata a lokacin bikin.

Bayan na gabatar da jawabai, Emine Erdogan ta karɓi lambar yabon ‘Jagora Mace da Ta yi Zarra ‘ daga Taron Ba Da Tallafi na Duniya.

A baya dai ta karɓi lambar yabon Jinƙai a shekarar 2018 domin gwagwarmayarta, musamman game da matsalar Musulmai ‘yan ƙabilar Rohingya.

Taron Masu Ba da Tallafi na Duniya, da aka fara yi a shekarar 2008, na da zummar tattaro albarkatun kuɗi da da ilimi  domin samar da duniya mai adalci da zaman lafiya fiye da shingen ƙabila ko addini.

Taron ya samu halartar manyan mutane ciki har da ɗan majalisar Birtaniya Naz Shah da mataimakkin magajin garin Landan Paul Palmer da kuma minister harkokin wajen Afirka ta Kudu Naledi Pandor.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us