Me ya faru a cibiyar rabon kayan agaji ta Gaza?
Me ya faru a cibiyar rabon kayan agaji ta Gaza?
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa rabon kayan agaji da Asusun Jin Kai na Gaza ke yi, wanda Amurka da Isra’ila ke goyawa baya, na fuskantar hatsarin kawar da shi daga wuraren da aka fi bukatar agaji a yankin na Falasdin.
28 Mayu 2025

A ranar Talata, Asusun Agaji na Gaza da Amurka da Isra’ila ke goya wa baya sun fara rabon kayan agajin jin kai a wata cibiya da ke kudancin Gaza.

An samu hargowa da cunkoso a yayin da dubunnan Falasdinawa suka ruga zuwa cibiyar da ke Rafah, in ji dan jaridar AFP da mahukuntan yankin.

“Jiya mun ga hotuna da bidiyo masu razanarwa na masu jin yunwa da ke tura katanga, suna neman abinci. An samu cunkoso da hargowa, babu daraja da tsaro,” in ji shugaban Hukumar MDD d ake kula da ‘yan gudun hijirar Falasdin (UNRWA) Philippe Lazzarini a Tokyo.

Lamarin na zuwa ne kwanaki bayan bayan an dan bude hanyoyin kai kayan agaji a kan iyakokin da Isra’ila ta toshe hanyoyin shiga a ranar 2 ga Maris, wanda ya janyo tsananin karancin abinci da magunguna.

Harba bindigu

Ma’aikatar Lafiya ta Falasdin da ke Gaza ta ce a kalla an kashe mutum guda yayin da wasu 48 suka jikkata a lokacin da dakarun Isra’ila suka bude wuta a kan dandazon mutanen da suka ci karfin wajen bayar da taimakon a Gaza.

Tun da fari, ofishin kare hakkokin dan adam na Majalisar DInkin Duniya a ranar Laraba ya ce an jikkata wasu mutane a lokacin da ake turmutsutsun karbar abinci a ranar Talata a wajen rabon kayan taimakon a Gaza da ke karkashin GHF.

“An jikkata mutane 47 saboda harbin bindiga,” Ajith Sunghay, Shugaban Ofishin Kare Hakkokin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya a Yankunan Falasdinawa da Aka Mamaye, a yayin tattaunawa da manema labarai a Geneva, inda ya ce ya samu bayanai daga abokan aiki da ke wajen.

Ya ce “Dakarun Sojin Ista’ila ne suka yi harbin bindigar.”

Ofishin kare hakkokin dan adam na MDD din bai bayyana takamaiman wajen da aka jikkata mutanen ba.

‘Rashin nasara mummuna’

A gefe guda, Amurka na ikirarin raba kayan abinci ga dubunnan daruruwan Falasdinawa da ke tsananin bukata.

Kakakin Ma’aikatar Tsaro ta Amurka Tammy Bruce a ranar Talata ya shaida cewa kungiyar tallafin ta hadin gwiwar Amurka da Isra’ila ta bayar da tan 462,000 na abinci a cikin akwatina 8,000.

Bruce ya ki cewa komai game da rahotannin cewa sojojin Isra’ila sun kai hari kan Falasdinawa da ke gudu zuwa wajen rabon taimakon a garin Rafah na kudancin Gaza, maimakon haka sai ya mayar da hankali kan nasarar raba abincin da kungiyar ta yi.

Ofishin Kafar Yada Labarai ta Falasdin a Gaza, ta fitar da sanarwa a wannan rana, ta ce “Shirin tallafi na mamayar Isra’ila a yankin tattara mutane ya baci tare da munana.”

Jefa bukatun jinƙai cikin hatsari

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya Mai Kula da Harkokin Jin Kai (OCHA) ya yi gargadin cewa raba kayan taimakon da GHF ke yi na fuskantar hatsarin barin ind aake tsananin bukatarsa a Gaza.

An kasa Asusun taimakon a watan Fabrairu, kuma Majalisar Dinkin Duniya ta soke shi sosai, wanda jami’anta suka ce shirin rarraba kayayyakin zai tirsasa sauya matsugunin Falasdinawa da kara kawo yamutsi.

Wata kungiya mai sanya idanu kan yunwa a duniya ta yi gargadin cewa sama da rabin miliyan na mutane a Gaza na na fuskantar hatsarin yunwa, kashi daya bisa hudun jama’ar yankin.

Isra’ila ta hana kai kayan abinci, magunguna da tallafin jin kai zuwa Gaza tun 2 ga Maris, wand ahakan ya kara tsananta mummunan halin d aake ciki a yankin, wand ake shafar ‘yan Gaza su miliyan 2.4.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us