Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Italiya, FIGC, ta sanar da jinkirta wasannin gasar gasannin Serie A, B, da C, saboda alhinin rasuwar shugaban ɗarikar Katolika, Fafaroma Francis.
Ƙungiyoyin da dakatarwar ta shafa sun haɗa da Juventus, Lazio, Parma Calcio, Cagliari, Fiorentina, Genoa, Torino, Udinese.
A safiyar Litinin 21 ga Afrilu ne Fadar Cocin Katolika da ke Vatican City ta sanar da rasuwar Fafaroma Francis mai shekaru 88, wanda ke shugabantar Cocin, kuma shugaban birnin Vatican City.
Miliyoyin mutane a Italiya da kuma faɗin duniya sun shiga alhini saboda rasuwar malamin adinin. Wannan ya sa an ɗauki matakin jingine duka lamuran wasanni don nuna girmamawa ga rasuwar.
Shugaban hukumar FIGC, Gabriel Gravina ya ce, “Harkar ƙwallon ƙafa ta Italiya tana taya jimami ga miliyoyin al’umma kan rasuwar Mai Alfarma Fafaroma Francis.
Jimamin masoya ƙwallo
Gravina ya ƙara da cewa, “Kusancinsa da al’umma, da imaninsa, da kyautatawa majinyata, da talakawa da waɗanda aka zalunta a faɗin duniya su ne shaidarsa…, Za mu tuna shi har abada a zukatanmu na masoya wasan ƙwallon ƙafa.”
An soke duka wasannin da aka shirya bugawa ranar Litinin ta Easter. A babbar gasar Serie A ta Italiya, Juventus za ta kara da Parma, Lazio da Genoa, Torino da Udinese, Cagliari da Fiorentina.
Haka ma a ƙananan gasannin Italiya na Serie B da Serie C su ma an soke buga wasannin da aka tsara a baya.
Tarihi ya nuna cewa ko a 2005 da Fafaroma John Paul II ya rasu, an ɗauki irin wannan mataki.
Zuwa yanzu ba a fitar da sabon jadawalin wasannin da za a buga ba. Yawancin ƙungiyoyin suna da sauran wasanni biyar ne kafin kammala kakar gasanni ta bana.