Girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 6.2 ta afka wa gundumar Silivri da ke birnin Istanbul na ƙasar Turkiyya, in ji hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasar (AFAD).
Girgizar ƙasar ta faru ne da misalin ƙarfe 12.49 na rana na ƙasar (misalin ƙarfe 0949 a agogon GMT) kuma an ji girgizar a faɗin Istanbul ranar Laraba da kuma jihohi masu maƙwabtaka, lamarin da ya sa mazauna birnin suka tsere cikin tsoro.
An kuma samu wata girgizar ƙasar mai ƙarfin maki 4.9 da misalin ƙarfe 1.02 na rana a ƙasar (misalin ƙrfe 10:02 na safe agogon GMT), wanda ya auku a kusa da tekun Buyukcekmece a kogin Marmara.
AFAD ta ce an tattara dukkan hukumomi da jami’ai masu ba da agaji kuma an fara gwaje-gwaje domin gano ɓarnar ko kuma tsaron jama’a.
Hukumar ta jaddada cewa jami’a suna sa ido kan lamarin kuma suna jagorantar matakai bisa lamarin. Ba a samu rahoton mutuwa ko rauni ba nan-take ko kuma wata babbar ɓarna.
A wata sanarwa, Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce hukumomi suna sa ido kan yadda lamarin ke wakana.