Kyaftin din tawagar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya kuma ɗan wasan Kano Pillar ta jihar Kano, Ahmed Musa ya samu sabon muƙami a jihar tasa.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa Ahmed Musa a matsayin sabon janar manajan ƙungiyar ƙwallo ta jihar, wato Kano Pillars.
Sanarwar naɗin ta fito ne ranar Juma’a 4 ga Yuni daga bakin kakakin gwaman, Sunusi Bature Dawakin Tofa.
Ahmed Musa mai shekaru 32 shi ne kyaftin ɗin tawagar Super Eagles ta Nijeriya, duk da dai bai faye buga wa ƙungiyar wasanni ba a ‘yan shekarun nan.
Masu nazari kan harkokin ƙwallo a Nijeriya na ganin wannan sabon muƙami zai iya zama dadlilin da Ahmed Musa zai yi ritaya daga ƙwallon ƙafa.
Ɗan wasan dai ya taka rawa sosai a harkokin ƙwallo da cigaban matasa a ƙasar, kuma a yanzu yana buga wa ƙungiyar ta Kano Pillars wasa bayan dawowarsa Nijeriya da buga ƙwallo.