Yayin da sabon kocin Real Madrid, Xabi Alonso ke nuna alamun barin matashin ɗan wasan gaba na Real Madrid, Rodrygo, rahotannin na cewa an saka wa ɗan wasan farashi ga ƙungiyoyin da ke tayin sayan sa.
Farashin da Madrid ta saka wa ɗan wasan ɗan asalin Brazil ya kai euro miliyan €90 (dala miliyan $104), kuma zuwa yanzu Arsenal ce ke kan gaba a maneman nasa.
Rodrygo dai bai samu buga duka wasannin da tawagar Real Madrid ta yi ba zuwa yanzu a gasar kofin duniya na kulob-kulob, ƙarƙashin sabon koci Alonso.
A gasar da ke gudana a biranen Amurka, Rodrygo ya buga wasan farko na Real Madrid da Al-Hilal, amma sai koci Alonso ya bar shi a benci a wasa na biyu da suka doke Pachuca ta Mexico.
Zuwa yanzu kuma ta tabbata a fili cewa Real Madrid na fatan sakin ɗan wasan, domin samun damar nemo sabon ɗan wasan tsakiya da zai maye gurbinsa a tawagar.
Arsenal ko Man City?
Masu bibiyar cinikayyar ‘yan wasa a Turai suna ganin Rodrygo na dab da komawa Arsenal, kasancewar koci Mikel Arteta na ƙoƙarin ƙarfafa ‘yan wasansa na gaba.
Da ma an daɗe ana raɗe-raɗin cewa Rodrygo zai bar Madrid, duk da a baya an jiyo Alonso na cewa yana fatan ɗan wasan zai ci gaba da zama a Madrid.
Sai dai ganin yadda Alonso ya zaɓi saka ‘yan wasan gaba Gonzalo Garcia da Brahim Diaz a wasansu da Pachuca, dole Rodyrygo ya sake tunani kan makomarsa.
Baya ga Arsenal, Manchester City ma na cikin ƙungiyoyin da ke sha’awar ɗauko Rodrygo tun bazarar bara, kuma a yanzu ma an ce sun sake shirin nemo shi.
Sai dai abin lura shi ne, akwai sauran shekaru uku a kwantiragin Rodrygo da Real Madrid, kuma ya taimaka wajen cin ƙwallo guda da Madrid ta ci Al-Hilal ta Saudiyya ranar 18 ga Yuni a wasan da aka tashi 1-1.