Ramadan: Me ya sa ake ta magana kan buɗa-bakin da Dangote ya yi da Burna Boy
Ramadan: Me ya sa ake ta magana kan buɗa-bakin da Dangote ya yi da Burna Boy
Masoya waƙoƙi sun rinƙa jinjina wa shahararren mai kuɗin nan na Afirka Aliko Dangote a kafafen sada zumunta bayan ya gayyaci Burna Boy buɗa-baki.
2 saat əvvəl

Aliko Dangote, wanda shi ne wanda ya fi kowa kuɗi a Afirka, ba wai shahararren ɗan kasuwa ne ba kawai, amma ya kasance mai son ƙula alaƙa ta ɓangaren addini.

A wannan makon, ya buɗe ƙofofinsa domin buɗa-baki, inda ya gayyaci mawaƙin nan Burna Boy da kuma mai ruwa da tsaki a harkokin waƙoƙi Cecil Hammond da kuma wasu abokan arziki zuwa buɗa-baki.

A wani bidiyo da ya yi yawo a shafukan sada zumunta, an ga shahararren mai kuɗin da wasu mutanen a gefen teburi a daidai lokacin da suke shirin yin buɗa-bakin azumi na huɗu na watan Ramadan.

Wasu daga ciki sun nuna muhimmancin yin irin wannan taron wanda suka ce zai taimaka wurin haɗin-kan addinai sakamakon su mawaƙan da aka gayyata ba Musulmai ba ne.

Ceceil Hammond, wanda ya saka hoton buɗa-bakin, ya rubuta “Haɗa shahararru a wuri guda, murmushi ɗaya a lokaci guda.”

Kyakkyawar dangantaka

Abin sha'awa, Burna Boy ya yi wata waƙa ɗaya mai taken 'Dangote' a shekarar 2019 daga cikin fitaccen kundinsa ''Giant Africa''.

Duk da cewa waƙar ba wai kai-tsaye a kan Dangote ya yi ta ba, amma ya yi amfani da sunan attajirin a matsayin wata alama ta buri da arziki.

Bisa kididdigar arziki da Mujallar Forbes ta yi, Dangote a halin yanzu shi ne mutum mafi arziki a Afirka da dala biliyan 23.9, sannan shi ne na 86 a duniya.

Tun bayan fitar da bidiyon, magoya bayan Dangote sun yaba wa attajirin a shafukan sada zumunta kan yadda ya rika ‘dinke barakar da ke tsakanin tsararraki’.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Dangote ke irin wannan taro da mawaƙa ba. A baya, ana ganinsa tare da fitattun mutane a harkar waka, ciki har da fitaccen mawakin Nijeriya Davido.

Wannan taro na buda baki da Burna Boy ya biyo bayan wani gagarumin taro da hamshakin attajirin nan na Nijeriya, Femi Otedola, ya karbi bakuncin Burna Boy, Hammond, da Wizkid a gidansa a ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu, abin da aka kira liyafar kasuwanci.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us