Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja Babban Birnin Nijeriya ta bayar da umarnin ci gaba da tsare wasu ‘yan ta’adda uku daga cikin mutum takwas da ake zarginsu da alaka da ƙasurgumin ɗan fashin dajin nan Bello Turji a gidan yarin Kuje.
A ranar Litinin ne Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da mutanen a gaban kotun bisa zargin aikata laifukan ta’addanci, ko da yake sun musanta tuhume-tuhume 11 da ake zarginsu da aikatawa.
Ana zargin waɗanda ake tuhuma ne da samar da haramtattun kayayyaki aiki ga ƙungiyoyin ta'addanci ƙarƙashin jagorancin Bello Turji da Kachalla Halilu da Danbokolo, da Lawali, da Atarwatse, da Buderi da dai sauransu, daga ciki har da miyagun ƙwayoyi da tabar wiwi da kayan abinci, kayan soji da na 'yan sanda da makamai.
Kazalika ana zarginsu da samar da takalma da huluna da kayayyakin gini da buhunhunan siminti da ƙusoshi da sanduna da sauran kayayyaki ga sansanonin ‘yan ta’adda da ke dazuzzukan jihohin Zamfara, da Sokoto, da kuma Kaduna.
NIJERIYA
1 minti karatu
Labaranmu Na Yau, 24 ga Disamban 2024
Wata babbar kotu a Abujan Nijeriya ta umarci a ci gaba da tsare mutanen da ake zargi da alaka da gawurtaccen dan ta’addan nan Bello Turji sannan Majalisar Dinkin Duniya ta ce Gaza ita ce wuri mafi hadari wajen isar da kayayyakin jinkai.
Labaranmu Na Yau Thumb nail / TRT Afrika Hausa
25 Disamba 2024
Rumbun Labarai