Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya umarci hakimansa da su yi shirin yin Hawan Babbar Sallah da ke zuwa a cikin makon nan.
A wata sanarwa mai ɗauke a sa hannun Damakwayon Kano Alhaji Abba Yusuf, wacce aka fitar ranar Talata, sanarwar masarautar ta ce ana umartar dukkan hakimai su shiga cikin birnin Kano tare da mahayansu da dawakansu ranar Laraba, jajiberin Hawan Arfa.
Wannan na zuwa ne bayan dambarwar da aka sha a kan atun Hawan Sallah lokacin bikin Ƙaramar Sallah da aka yi a watan Maris.
A wancan lokacin hukumomin tsaro sun dakatar da masarautar daga yin duk wani abu da ya shafi hawan sallah “don guje wa tayar da hargitsi” kamar yadda suka ce.
Labari mai alaƙa: ‘Yan sanda sun gayyaci Sarkin Kano Muhammadu Sanusi Abuja don amsa tambayoyin kan 'Hawan Sallah'
Kazalika a wannan sabuwar sanarwar, Majalisar Masarautar ta ce ana kuma neman hakiman su hallara a Fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu a ranar Alhamis don karɓar umarnin Sarki.
“Sai kuma bayan tashi daga Majalisar Sarki za a yi wani taron a dakin taro na Majalisar Masarautar Kano don yi muku bayanin yadda hawan zai kasance.”
A ƙarshe Majalisar Masarautar ta ce ta sanar da shugabannin ƙananan hukumomin dukkan Hakiman don a taimaka wa hakiman wajen shiga Kano yin Hawan Sallar.