Aƙalla mutum 11 ne suka rasu sakamakon hare-haren ƙungiyar da ke iƙirarin jihadi ta ISWAP ta kai a garin Malam Fatori da ke kan iyakar Nijeriya da Nijar.
Mai magana da yawun rundunar haɗin gwiwa ta MNJTF Laftanal Kanal Olaniyo Osoba ya bayyana cewa mayaƙan sun kai hari ne kan wani sansanin ‘yan gudun hijira inda suka buɗe wuta kan jama’ar da ke sansanin na Jihar Borno.
"Yan ta'addan ISWAP sun kai hari Malam Fatori da safe. Sun kashe mutum 11, amma yanzu dakarun soja sun karɓe iko da yankin,” in ji Laftanal Kanal Olaniyo Osoba.
Rundunar MNJTF, wadda haɗaka ce ta dakarun ƙasashen Nijeriya da Nijar da Chadi da Kamaru ce, an kafa ta a shekarar 1998 domin yaƙi da laifukan kan iyaka, amma daga baya aka fadada aikinta zuwa yaƙar 'yan ta'adda a yankin.
Fiye da mutum 40,000 ne suka mutu, kuma fiye da mutum miliyan biyu ne suka rasa matsugunansu a arewa maso gabas sakamakon hare-haren masu iƙirarin jihadi da suka shafe shekara 16 suna kaiwa.
Wani dan ƙungiyar fararen hula masu yaki da ta'addanci, Abor Mallum, wanda ke taimaka wa sojoji, ya bayyana cewa mayaƙan sun shiga cikin garin da motoci ɗauke da bindigogi masu sarrafa kansu da misalin karfe 12:20 na dare, inda suka kai farmaki kan sansanin da ke ɗauke da dubban ‘yan gudun hijira.
Mallum ya ƙara da cewa maharan sun ƙona asibiti da gine-ginen gwamnati kafin su janye daga yankin, inda ya ce waɗanda suka mutu sun kai 12, tare da raunata wasu 20 da aka garzaya da su asibiti a Bosso da ke Nijar.
Garin Malam Fatori, wanda ke da tazarar kilomita 200 daga birnin Maiduguri babban birnin Jihar Borno, an ƙwace shi daga hannun Boko Haram a shekarar 2014, amma sojojin Nijeriya suka sake ƙwato shi a 2015.
Sojojin Nijeriya sun kafa sansanin soja a garin kuma sun daƙile hare-hare da dama daga kungiyar ISWAP, wadda ta ɓalle daga Boko Haram a 2016 tare da mayar da yankin Tafkin Chadi matsuguninta.